Rashin kungiyar ko da na wucin-gadi ne, zai kara ta'azzara mummunan halin da yaki ya tagayyara yake ciki, a lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan samun yunwa a yankin.. / Hoto: AP

World Central Kitchen, kungiyar bayar da agaji da sananne Jose Andres ya kafa, ta yi kira ga dakatar da ayyukanta a Gaza bayan an kashe sojojinta bakwai a harin da Isra'ila ta kai.

Kungiyar, wadda ta ce za yi nazari kan dadewa a yankin, ta kasance tana bayar da abinci ga Falasdinawa mabukata da ke Gaza, wadanda suke fuskantar matsananciyar yunwa, kuma ta samar da hanyar kai kayan taimako ta bangaren tekun Kudancin Cyprus.

Rashin kungiyar ko da na wucin-gadi ne, zai kara ta'azzara mummunan halin da yaki ya tagayyara yake ciki, a lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan samun yunwa a yankin.

Wace kungiya ce World Central Kitchen?

An kafa kungiyar ta World Central Kitchen a 2010, kuma tana bayar da taimakon dafaffe da ɗanyen abinci ga mabukata a yankunan da wani ibtila'i ya afka wa, kamar guguwa ko girgizar kasa, ko wadanda yaki ya tagayyara.

Kungiyar tana kuma samar da abinci ga 'yan gudun hijira da suke zuwa iyakar kudancin Amurka, da ma ma'aikatan asibitoci da ke aiki a lokacin annobar korona.

Kungiyar bayar da tallafin na aike wa da ma'aikata da suke dafa abinci a yankunan da za a taimaka wa.

"A lokacin da ka yi magana game da abinci da ruwa, mutane ba sa son a ce sai nan da mako daya ko wata daya za a warware matsalar, yanzu-yanzu suke so a magance ta," in ji Ander a wata sanarwa da ya fitar a shafin yanar gizon kungiyar.

World Central Kitchen ta yi aiki a gomman yankunan da rikici ya shafa ko yake shafa a yanzu kuma suna da tawaga a Haiti, suna kokarin magance matsalolin jama'ar Ukraine da yakin Rasha ra baa da matsugunanu, sannan suna a aiki a Gaza don agazawa wadanda hare-haren Isra'ila suka shafa.

Me ta yi a lokacin yakin Gaza?

Tawaga daga kungiyar ta rinka zuwa yankunan Gaza tun bakwai ga Oktoba. Ta ciyar da 'yan Isra'ila da rikici ya raba da matsugunansu, haka ma tsaffin fursunonin yaki, kamar yadda shafin yanar gizonta ya sanar, kuma suna ciyar da mutane a Labanan da yaki ya tagayyara a Isra'ila. Amma aikin da take yi a Gaza ne abin da aka fi bukata.

A Gaza, kungiyar ta bayyana samar da abinci sama da kwano miliyan 43 ga Falasdinawa.

Kungiyar na aiki a dakunan girki biyu Rafah da Deir al Balah, suna taimaka wa unguwanni 68 da ke Gaza, suna bayar da kunshin abinci sama da 170,000 kowace rana, suna raba kwalayen kayan abinci 92,000, wanda jumullar ya kama abincin mutum miliyan 4.7

Kungiyar ta kara yawan ayyukanta a Ramadan, wata mai tsarki da Musulmai suke azumi a cikin sa, inda kungiyar ta raba manyan kwalaye 92,000 na kayan abinci.

Kungiyar ta kuma samar da kayan abinci ta hanyar mika su ga mabukata ta jiragen sama da na ruwa a arewacin Gaza, inda aka fi bukatar abincin.

A wata tattaunawa da aka yi a watan da ya gabata, Andres ya bayyana dalilin da ya sanya suka kai kaya ta teku zuwa Gaza da zaburar da Amurka kan ta fitar da hanya ta teku da za a dinga kai taimako ga Gaza ta tekun.

Ya ce "Ina tunani wannan babban ci gaba ne a wajen mu."

Me rashin wanzuwar kungiyar a yankin zai yi ga Gaza?

A yayin da World Central Kitchen ke dakatar da ayyukanta a Gaza, ba za a samu damar bayar da abinci a yankin ba.

Bayan mummunan harin da aka kai, Gwamnatin Tsibirin Cyprus bangaren Girka ta ce kayan abincin da suka zo ta teku zuwa Gaza za su dawo tsibirin na Bahar Rum dauke da tan 240 na kayan abinci. An sauke kusan tan 100, in ji kakakin gwamnatin.

Sauran kungiyoyin agaji na nan na bayar da kayan taimako ga Falasdinawa, ciki har da Majalisar Dinkin Duniya, amma kungiyoyin agajin na cewa ba a iya kawo kaya yanzu zuwa Gaza yadda ya kamata, kayan na fuskantar matsaloli saboda yakin da ake ci gaba da yi.

Isra'ila ta musanta cewa akwai karancin abinci a Gaza, kuma ta dora laifi kan Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin bayar da agaji saboda gazawar su wajen kai kaya zuwa cikin jama'a sosai.

World Central Kitchen na kan bakarta domin ganin ta mika kayan da ke cikin jiragen ruwa da suka isa Gaza kwanan nan. Ba a san me zai ci gaba da wakana ba a yankin saboda babu kungiyar, inda Amurka kuma ke shirin samar da hanyar kai kayan agajin.

TRT World