| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
Trump ya yi gargaɗin cewa yaƙi da Iran zai zo ƙarshe ko ta halin ƙaƙa 'nan ba da jimawa ba’
Shugaban Amurka ya nuna cewa ana gab da tsayar da matsaya kan daukar karin matakan soji ko kuma cim ma yarjejeniya da Tehran.
Trump ya yi gargaɗin cewa yaƙi da Iran zai zo ƙarshe ko ta halin ƙaƙa 'nan ba da jimawa ba’
Shugaban Amurka ya nuna cewa ana gab da tsayar da matsaya kan daukar karin matakan soji ko kuma cim ma yarjejeniya da Tehran.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce dole ne ya yanke shawara kan ko zai ci gaba da yaƙi da Iran ko kuma ya cim ma yarjejeniya, yana mai nuna cewa yana dab da yanke hukunci ba tare da bayyana matakin da zai ɗauka na gaba ba.

Da manema labarai suka tambaye shi ranar Laraba kan yadda yake shirin ɗaukar mataki game da jami'an Iran, Trump ya amsa da cewa: "Wataƙila a ruguza su."

"Dole ne mu yanke wannan shawara: Mu ruguza su ko mu cim ma yarjejeniya," in ji Trump, yana mai ƙari da cewa "Amma lokaci yana zuwa. Zai ƙare nan ba da jimawa ba, ko ta halin ƙaƙa."

Shugaban Amurka ya nuna cewa ana gab ɗaukar matsaya kan ƙarin matakan soja ko kuma cim ma yarjejeniya da Tehran.

Cikin ‘yan makonnin nan, Trump ya sha faɗin cewa yana nazari kan ɗaukar ƙarin matakan soja ko kuma ya cim ma yarjejeniyar da Tehran.

Kazalika Shugaban na Amurka ya musanta rahotannin kafofin watsa labarai na baya bayan nan da ke cewa yana son ba da sassaucin takunkumin tattalin arziki da kuma sakin kuɗaɗen da aka hana amfani da su na Iran don musanya da shirin nukiliyarta.

"Wuce-gona-da-iri"

Kafofin watsa labaran Amurka Axios da CNN sun ruwaito a ranar Litinin cewa shugaban Amurka ya ba Iran sassaucin takunkumi da kuma sakin kuɗaɗen da aka dakatar, yayin da yaƙin Gabas ta Tsakiya ke ci gaba da ƙara zafi.

"Axios ya fitar da wani labari da ke cewa 'Trump' ya bayar da sassauci ga takunkumi da kuma kudaden da aka riƙe ga Iran. Wannan ba gaskiya ba ne. Ban ba su KOMAI BA!" kamar yadda Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social.

A ƙarshen mako, shugaban Amurka ya yi watsi da shawarar Iran wadda ta mayar da hankali kan sassauta rikicin da sake buɗe Mashigar Hormuz, yana mai bayyana buƙatar Tehran da wanda "ba za a yarda da shi ba" a yanayin yakin Iran na watanni bakwai.

Trump ya fada a karshen makon nan cewa, yana sa ran karin tattaunawa da Tehran, kana ya yi ikirarin cewa jami'an Iran sun "wuce-gona-da-iri" a lokacin tattaunawarsu ta baya.

Rumbun Labarai
Trump ya yi wa Iran barazana, ya kira ICC ‘marar gaskiya‘, ya sauya sunan AI zuwa ‘SI’
Amurka ta kai 'yan ci-rani fiye da 25,000 da ta kora zuwa ƙasashen da ba su da alaƙa da su: Bincike
Antonio Guterres ya nemi a bai wa Afirka kujerun dindindin a Kwamitin Tsaro na MDD
Trump ya sa hannu kan sabuwar dokar takunkumi ga Rasha: China da India na iya fuskantar sabon haraji
Kasashen Yamma na shirin yaƙi da Rasha: Lavrov
Ƙanwar Kim Jong-un ta ce 'wawaye' ne kawai ke tunanin Koriya ta Arewa za ta miƙa makaman nukiliyarta
Taliban na neman ƙulla dangantaka da Amurka da sharaɗin a duba illolin yaƙin Afghanistan
Wuta za ku je idan ba ku jefa ƙuri'a a zaɓen 'yan majalisa ba, in ji Trump ga 'yan Republican
Shekaru 25 bayan 9/11, Amurkawa na tsoron ta’addancin cikin gida fiye da barazanar hari daga waje
Turkiyya da kasashe 7 sun yaba wa Birtaniya kan hana kawo kaya daga haramtattun mazaunan Isra'ilawa
An samu sojojin Jamus da laifuka kusan 2,000 da suka shafi cin zarafi ciki har da lalata da yara
Koriya ta Arewa ta yi alƙawarin kafa rundunar sojin ruwa mai amfani da makaman nukiliya
Faɗaɗa Yarjejeniyar Makka: Me Bangladesh za ta iya kawo wa ƙawancen?
Kotu a Las Vegas ta samu tsohon jagoran 'yandaba Duane 'Keffe D' Davis da laifi a kisan Tupac Shakur
Cizon sauron da suka shiga Jamus ta jirgin sama ya kashe ma'aikatan filin jirgi biyu
Tsananin zafi ya yi ajalin mutane 15,800 a Jamus a bazarar bana
Shugaban hukumar leƙen asiri ta Rasha ya tabbatar da ganawa da Shugaban CIA a Moscow
Ambaliya da zaftarewar ƙasa a Nepal sun yi ajalin gommai da ɓatar da ɗaruruwa a kusa da iyakar China
Trump ya gabatar da yarjejeniyar shekaru 30 ta haɗin gwiwar nukiliyar Saudiyya ga Majalisar Amurka
Mummunar guguwa ta katse wutar lantarki a gidaje 26,000 a kudu maso-gabashin Faransa