| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
Trump ya ce rashin ba shi kyautar Nobel ta Zaman Lafiya 'abin kunya ne'
Shugaban ya shaida wa wani gangami na magoya bayansa a Syracuse na New York cewa Amurka "wadda nake wakiltarta a matsayin shugabanku, ita ta dace ta samu kyautar Nobel ta Zaman lafiya, amma ba ta samu ba."
Trump ya ce rashin ba shi kyautar Nobel ta Zaman Lafiya 'abin kunya ne'
Trump yana kamfe wa ɗantakaran gwamnan New York a jam'iyyar Republican, Bruce Blakeman, da sauran 'yantakaran jam'iyar a zaɓen rabin wa'adi na Nuwamba

Shugaban Amurka Donald Trump ya soki "abin kiunya" na zaɓar wadda aka bai wa kyautar Nobel ta Zaman Lafiya a matsayin abin da ya bar "dattin da ba za a iya gogewa ba" kan ƙasar Norway, yana mai cewa shi ya kamata a bai wa kyautar.

Alƙaliyar Afirka Ta Kudu kuma mai fafatukar kare haƙƙin bil Adama Navi Pillay ce ta lashe kyautar ranar Jumma’a bisa aikin da ta yi kan yaƙi da laifukan yaƙi da kuma laifuka kan bil Adama.

Amma Trump ya bayyana zaɓin kwamitin kyautar Nobel ɗin na Norway a matsayin "hukunci na kunya mai kunyatarwa", inda yake sanar da wani gangamin magoya bayansa a Syracuse, New York cewa shi "bai taɓa jin [sunan]" Pillay ba.

"Ban taɓa jin [sunan] wannan mutumiyar ba, amma koma me ne ne ina taya ta murna," in ji shi.

"Amurka, wadda nake wakilta a matsayin shugabanku, ita ce ya kamata ta sami kyautar Nobel ta Zaman lafiya, amma ba ta samu ba ."

Ya ce zaɓin Pillay a matsayin wadda ta ci kyautar ya bar "wani datti da ba za a iya gogewa ba a kan ƙasar Norway".

Tun da ya koma fadar White House a watan Janairun shekarar 2025, Trump bai ɓoye sha’awarsa ta lashe kyautar Noble ta Zaman lafiya ba.

Ya lisaffa rikice-rikicen da shi ya taka rawa wajen warware su kuma ya ce shi ya taimaka wajen hana yaƙe-yaƙe ɓarkewa tsakanin Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu da Japan da Koriya ta Arewa da kuma China da Taiwan.

Ba za mu manta ba — Trump

Kyautar na zuwa ne da lambar yabo ta zinari da takardar shaida da kuma kuɗi da ya kai dala miliyan $1.2.

"Kyautar Nobel ta Zaman Lafiya tana ta samun zagon ƙasa daga wasu masu tsauraran ra’ayi da ke cusa aƙidu waɗanda ke ƙin dimokuraɗiyya kuma suna [kasancewa] maƙiyan wayewa. Kuma ba za mu manta ba, Norway," in ji shi.

Pillay ta yi raha game da bai wa Trump daga cikin kyautarta, inda ta sanar da wani taron mutane da suka tafa mata bayan an yi shelar kyautar cewa: "Idan kuka ƙara tafi, zan iya bai wa Trump daga cikin wannan kyautar."

Da alama wannan tsokanar ta yi ta ne ga ‘yar adawar Venezuela Maria Corina Machado, wadda ta ba da lambar yabon zinari na kyautar Nobel ɗinta ga Trump bayan ta lashe kyautar a shekarar da ta gabata.