Hukumomin Iran sun kama mutum 500 game da tuhume-tuhumen leƙen asiri tun da Amurka da Isra’ila suka fara kai mata hare-hare, kamar yadda babban hafsan ‘yansandan ƙasar ya bayyana ranar Lahadi
Birgediya Janar Ahmadreza Radan ya ce waɗanda aka kaman an kama su ne bisa zargin “yin leƙen aisri wa abokan gaba da kuma kafafan watsa labarai masu hamayya,” in ji kamfanin dillancin labaran Tasnim.
Radan ya ce 250 daga cikin waɗanda aka rufe “sun ba da bayanan sirri ga kafar watsa labarai da ke Landan ta Iran International, ciki har da bayanai game da wuraren da aka kai wa hari.”
An kuma alaƙanta waɗanda ake zargin da ƙungiyoyi masu makamai da kuma ƙoƙarin jirkita doka da oda, in ji shi, yana mai bayyana su a matsayin “masu leƙen asiri” da suka kwarmata bayanai “ga abokan gaba da kuma kafafen watsa labarai masu hamayya.”
Gwamnatin Iran ta bayyana gidan talabijin na Iran International TV a matsayar wata “ƙungiyar ta’aaddanci a shekarar 2022,” inda ta zarge ta da yaɗa labaran ƙarya game da zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a ƙasar da kuma zuga masu zanga-zangar domin su ta da zaune-tsaye, kuma ta yi shelar ƙwace duk kadarorin ma’aikatanta a Iran.
Kamen na zuwa ne yayin da Amurka da Isra’ila suka ci gaba da harinsu na haɗin gwiwa kan Iran da suka fara tun ranar 28 ga watan Fabrairu, inda suka kashe kimanin mutum 1,300, ciki har da jagoran addinin ƙasar na wancan lokacin Ali Khamenei.
Iran ta ɗau fansa da hare-haren jirage mara matuƙa da makamai masu linzami inda ta kai hare-hare kan Isra’ila da Jordan da Iraƙi da ƙasashen Larabawa na gaɓar teku, waɗanda ta ce tana kaiwa ne kan kayayyakin sojin Amurka, lamarin da ya janyo mace-mace da kuma lalata kayayyakin fararen hula da kuma shafar kasuwannin duniya da ma sufurin jiragen sama.









