Gasar AFCON ta 2025 da Hukumar CAF ke gudanarwa a Maroko ta kafa sabon tarihi a fannin cin ƙwallaye, inda ta zama mafi yawan ƙwallaye a tarihin gasar.
A wannan karon, an ci zunzurutun ƙwallaye 120 kafin buga wasanni biyu na ƙarshen gasar da za a yi ranakun Asabar da Lahadi.
Adadin ƙwallayen bana ya wuce na baya da ya tsaya a ƙwallo 102, da kuma wadda aka samu a gasar 2019 a Masar.
Wannan na nuna ƙaruwar fannin kai hari a wasa, da ingancin ƙwarewa, da ƙaruwar himmar tawagogi a faɗin nahiyar.
Tsofaffin manyan tawagogi a Afirka sun kasance a gaba wajen wannan ƙaruwar cin ƙwallo.
Senegal, Nijeriya, Maroko da Ivory Coast duk sun nuna kaifin kai hari, yayin da sabbin 'yanwasa suka yi kankankan da taurarin da aka riga saninsu.
Brahim Diaz na Maroko ne ke kan gaba a jerin masu cin ƙwallo da ƙwallaye biyar, abin da ya sa shi zama ɗaya daga cikin fitattun 'yan wasa a gasar.
Bayansa kusa-kusa akwai Mohamed Salah na Masar da Victor Osimhen na Nijeriya, wanda kowannensu ya zura ƙwallaye huɗu.
Tun da duka 'yan wasan za su buga wasan neman zuwa na uku ran Asabar, gasar neman Kyautar Zinari tana nan a buɗe.









