Hare-haren sama da Isra'ila ta kai ya hallaka mutane 91 a Zirin Gaza tun daga daren Talata, ciki har da yara 24, wanda jami'an Falasdinawa suka bayyana a matsayin keta yarjejeniyar tsagaita wuta.
Hukumomin kiwon lafiya a Gaza sun bayyana a ranar Laraba cewa mutane 28 sun mutu a daren da ya gabata yayin da sojojin Isra'ila suka kai hare-hare kan gidaje, motoci, da tantuna da ke ɗauke da 'yan gudun hijira, har ma da asibiti da ke cikin yankin da ake kira “layin rawaya.”
Ƙungiyar gwagwarmayar Falasdinawa, Hamas, ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa tana nan daram kan yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta jagoranta, wadda aka fara aiwatarwa tun ranar 10 ga watan Oktoba karkashin shirin manufofi 20 na Shugaba Donald Trump.
Manufar yarjejeniyar ita ce tabbatar da zaman lafiya a yankin, da sake gina wuraren da yakin ya lalata, da kuma kafa sabon tsarin mulki ba tare da Hamas ta kasance a matsayin mai iko kai tsaye ba.
Netanyahu ya ba da umarnin “hare-hare masu karfi”
Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta, Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ba da umarnin abin da ofishinsa ya kira “hare-hare masu karfi” a Gaza bayan rahoton kisan wani sojan Isra'ila.
Shugaba Trump ya bayyana a ranar Laraba cewa tsagaita wutar “ba ta cikin haɗari,” duk da cewa Isra’ila na ci gaba da kai hare-haren.
A cewar hukumomin Falasdinawa, yaƙin ƙare dangi da Isra'ila ke yi a Gaza ya hallaka fiye da mutane 68,500 tare da jikkata sama da 170,000 tun daga watan Oktoba 2023.













