An gano gawarwaki bakwai, kuma an ceto mutane 96 bayan da wani jirgin ruwa da ke ɗauke da ‘yan ci-rani ya kife cikin dare a gaɓar tekun Gambia, in ji ma'aikatar tsaro ta Banjul.
Jirgin ruwan, "ana zargin yana ɗauke da ‘yan ci-rani fiye da 200", in ji ma'aikatar a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, inda ta ƙara da cewa 10 daga cikin baƙin haure da aka ceto suna cikin mawuyacin hali kuma suna samun kulawar gaggawa ta likita.
Sanarwar ba ta yi bayani kan sauran ‘yan ci-rani da ke cikin jirgin ba yayin da ake ci gaba da ayyukan ceto.
‘Yan gudun hijira da ke son zuwa Sifaniya na bi ta hanyar ta Tekun Atlantika daga Yammacin Afirka zuwa Tsibiran Canary, wadda ita ce mafi hatsari a duniya.
Fiye da ‘yan ci-rani ba bisa ƙa’ida ba su 46,000 sun isa Tsibirin Canary a shekarar 2024, a cewar Tarayyar Turai.
Fiye da mutane 10,000 ne suka mutu a yayin tafiyar zuwa Turai, kuma an samu ƙaruwar kashi 58 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar 2023, a cewar ƙungiyar kare hakkin bil'adama ta Caminando Fronteras.
A watan Agustan 2025, aƙalla mutane 70 ne suka mutu lokacin da wani jirgin ruwa da ake zargi ya tashi daga Gambia ɗauke da baƙin haure ya kife, a daya daga cikin haɗurra mafi muni a cikin 'yan shekarun nan.













