Kafofin yaɗa labarai na kasar sun bayar da rahoton cewa yan tawayen sun kashe mutane, sun yi garkuwa da wasu, kuma sun kwashe kayayyaki, sannan sun kona gidaje yayin da suke tserewa.
Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan hare-haren ta’addanci na baya-bayan nan da aka kai wa wuraren hakar ma’adanai a lardin Ituri da ke gabashin kasar.
An kai harin na baya-bayan nan ne a wurin hakar ma’adanai na Muchacha da ke yankin Mambasa a farkon wannan watan.
Gwamnati ta bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi cewa za ta bi sawun “miyagun da ke barazana ga tsaron jama’a har sai an dawo da cikakken ikon gwamnati a wannan yanki.”
A cewar gwamnatin, harin—wanda aka ɗora alhakinsa akan ƙungiyar ta’addanci ta ADF (Allied Democratic Forces)—ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, ya haddasa gobara a wurin hakar ma’adinan, sannan ya tilasta wa farar hula yin hijira.
Wadanda harin ya shafa
Kafofin yaɗa labarai na gida, sun ce ƙungiyoyin farar hula sun ce ’yan ta’addan sun kashe mutum bakwai, sun yi garkuwa da gomman mutane, sun kwashe kayayyaki, sannan suka kona gidaje lokacin da suke tserewa.
Sanarwar ta kara da cewa rundunar soji ta lalata sansanonin ADF da dama, sannan ta kwato bama-bamai masu yawa yayin da suke artabu da su a kwanan nan a lardin Ituri, musamman a yankin Mambasa.
Gabashin Kongo na daya daga cikin wuraren da hare-haren dakarun sa-kai suka fi yin kamari.
A makon da ya gabata, Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da ayyukan jin ƙai (OCHA) ya nuna matuƙar damuwa game da yadda ci gaba da tashe-tashen hankula ke shafar farar hula a lardin Ituri.
Tarihin Hare-hare
Masu yin hadin gwiwa na ayyukan jin ƙai sun bayar da rahoton cewa tun farkon watan Maris, fafatawa a ƙauyukan da ke kewaye da yankin Djugu ta yi sanadiyar mutuwar akalla mutum 21, sannan ta tilasta wa iyalai da dama barin gidajensu, in ji OCHA.
Tun daga shekarar 2021, dakarun Uganda da na Kongo suke gudanar da ayyukan haɗin gwiwa don yakar ’yan ta’addan ADF.
Kungiyar, wadda ta shafe shekaru tana gudanar da ayyukanta a gabashin Kongo, tana da alaƙa da Kungiyar Daesh (ISIS).
Ƙungiyar ce ta dauki alhakin kai hare-haren a wuraren hakar ma’adinan a ranar Asabar.
AFIRKA
2 minti karatu
Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo ta yi gargadi bayan hare-haren ta’addanci a wuraren haƙar ma’adanai
Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan hare-haren ta’addanci na baya-bayan nan da aka kai wa wuraren hakar ma’adanai a lardin Ituri da ke gabashin kasar.

Rumbun Labarai







