WASANNI
2 minti karatu
Dembele ya zama Musulmi baƙar-fata na farko da ya lashe kyautar Ballon d’Or
Dembele ne Musulmi baƙar-fata na farko da ya samu wannan kyauta.
Dembele ya zama Musulmi baƙar-fata na farko da ya lashe kyautar Ballon d’Or
Ɗan wasan PSG Ousmane Dembele ya lashe kyautar Ballon d’Or ta maza ta shekarar 2025 a bikin ba da kyautar ta 69 da aka yi a birnin Paris. / AP
12 awanni baya

Ɗan wasan PSG Ousmane Dembele ya lashe kyautar Ballon d’Or bayan rawar ganin da ya nuna a Gasar Champions League a kakar da ta gabata, yayin da ’yar wasan Spain Aitana Bonmati ce ta lashe kyautar a ɓangaren mata wanda wannan ne karo na uku da ta lashe kyautar a jere.

Dembele, mai shekara 28, ya doke ɗan wasan Barcelona Lamine Yamal ya lashe wannan babbar kyautar wacce Lionel Messi da Cristiano Ronaldo suka kwashe tsawon shekaru suna lashe ta.

Dembele ne Musulmi baƙar-fata na farko da ya samu wannan kyauta.

Ko da yake Zinedine Zidane da kuma Karim Benzema waɗanda Larabawa ne Musulmai sun taɓa lashe wannan kyauta.

Kazalika tsohon Shugaban Ƙasar Liberia George Weah shi ne ɗan Afirka na farko da ya lashe kyautar ta Ballon d’Or .

Dembele wanda tsohon ɗan wasan Dortmund ne da Barcelona yana cikin ’yan wasan da suka taimaka wa Faransa ta lashe Gasar Kofin Duniya a shekarar 2018 a Rasha.

Kuma ɗan ƙwallon ya ci ƙwallaye 35 a duka wasannin da ya buga wa PSG a kakar da ta gabata.

Dembele ya nuna hazaka a PSG musamman bayan tafiyar Kylian Mbappe Real Madrid, PSG ta yi nasarar doke Inter Milan 5-0 a wasan ƙarshe da suka buga a Gasar Champions League kuma wannan karonsu na farko a tarihi da suka lashe katafaren kofin.

“A gaskiya ba ni da wani abu da zan fada. PSG ta ji dadin kakar da ta gabata sosai,” kamar yadda Dembele ya bayyana cikin hawaye lokacin da aka gabatar masa da kyautar da ya lashe a birnin Paris.

Ɗan ƙwallon ya ci gaba da cewa kocinsa Luis Enrique – wanda ya lashe kyautar kocin da ya fi ƙwarewa a bana – ya ce ya kasance kamar “uba ne a wajena.”

“Kyauta ce da ake ba mutum daya amma kuma kyauta ce tamu gaba daya,“in ji Dembele, wanda daya ne cikin ’yan wasan PSG tara wadanda aka zabo don lashe gasar.

Yamal mai shekara 18 wanda ya zo na biyu ya taba yin wasa tare da Dembele a Barcelona a shekarar 2023, ya lashe kyautar Kopa Trophy ta ’yan wasa ’yan kasa da shekara 21.