Kocin Manchester City Pep Guardiola ya yi kira da a tallafa wa mutanen da girgizar kasar da aka yi a Turkiyya da Syria a watan jiya ta shafa.
Guardiola, mai shekara 52, yana daya daga cikin manyan mutane da suka shiga shelar hada kudi domin taimaka wa mutanen da girgizar kasar ta tagayyara.
Ma’aikatar Matasa da Wasannin Turkiyya da Hukumar Kwallon Kafar Kasar da kuma gamayya kungiyoyin kwallon kafa da kuma kamfanin labarai na beIN Media Gro up suka kaddamar da gidauniyar tara kudin tallafin.
"A madadin Manchester City, muna so mu tura kudin ga mutanen da wannan ibtila’I ya shafa a Turkiyya da Syria," a cewar Guardiola, a wani sakon bidiyo da Hukumar Kwallon Kafar Turkiyya ta wallafa a Twitter.
"Don Allah idan kuna da abin da za ku yi sadaka da shi, ku kawo. Za mu yi wannan aiki ne a madadin Manchester City. Muna fatan kowa zai yi irin wannan tallafi," in ji Guardiola.


















