AFIRKA
4 MINTI KARATU
Zaben Nijeriya na 2023: An soma shari'a kan zaben da ya bai wa Bola Tinubu nasara
Sai dai Atiku Abubakar, Peter Obi da wasu 'yan takarar sun garzaya kotu inda suke kalubalantar zaben.
Zaben Nijeriya na 2023: An soma shari'a kan zaben da ya bai wa Bola Tinubu nasara
INECT ta ce Bola Tinubu  ya samu kashi 37 na kuri'un da aka kada a zaben Nijeriya na watan Fabrairu. Hoto/Getty
8 Mayu 2023

A ranar Litinin ne wata kotun sauraron kararrakin zabe a Abuja ta soma shari'a kan karar da jam'iyyun adawa a Nijeriya suka shigar kotu don kalubalantar zaben da aka yi wa Bola Tinubu a matsayin shugaban kasar.

An gudanar da zaben shugaban kasar ne a watan Fabrairu kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya, INEC, ta ayyana dan takarar jam'iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara inda ya samu kashi 37 na kuri'un da aka kada.

Dan takarar da ke biye masa shi ne Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP wanda ya samu kashi 29 yayin da dan takarar jam'iyyar Labour Peter Obi ya samu kashi 25.

Sai dai Atiku Abubakar, Peter Obi da wasu 'yan takarar sun garzaya kotu inda suke kalubalantar zaben.

Atiku ya bukaci kotu ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben ko kuma ta sa INEC ta gudanar da sabon zabe wanda shi da Tinubu za su fafata.

Ya ce idan ba haka ba, ya kamata kotu ta soke zaben gaba daya sannan a sake gudanar da zabe.

Atiku ya ce Tinubu bai samu yawan kuri'un da suka isa a ayyana shi a matsayin shugaban kasa ba kuma bai cacanci tsayawa takara ba lokacin da aka gudanar da zabe.

A gefe guda, Mr Peter Obi ya nemi kotun sauraren kararrakin zaben da ta soke zaben sannan INEC ta gudanar da sabo kuma kada ta bari Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima da jam'iyyar APC su shiga zaben.

Kazalika dan takarar na LP yana so kotu ta bayyana cewa Tinubu bai lashe zaben da kuri'u mafi rinjaye ba.

Haka kuma ya bukaci kotu ta kwace takardar shaidar yin nasara a zabe da INEC ta bai wa Tinubu, sannan ta ba shi Obi sabuwar shaidar lashe zaben shugaban Nijeriya.

Peter Obi ya yi zargin cewa an tafka magudi a zaben kuma ita kanta INEC ta ki yin biyayya ga dokarta inda ta sanar da sakamakon zabe kafin a gama sanya shi a na'urar tattara sakamako.

A nasa bangaren, zababben shugaban Nijeriya Bola Tinubu, ya gaya wa kotun cewa Peter Obi bai cancanci kalubalantar nasararsa a zaben shugaban kasar ba.

Ya ce ba a bi ka'ida ba wajen tsayar da Mr Obi a matsayin dan takarar shugaban kasa na LP.

Ya kara da cewa Peter Obi ya sauya sheka daga PDP zuwa LP kasa da wata daya kafin gudanar da zaben fitar da gwani na jam'iyyar.

Kazalika ya ce Atiku ba shi da hujjar da za ta sa a soke zabensa, yana mai bukatar kotun ta yi watsi da kararsa.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Hatsarin mota ya yi ajalin fiye da mutum 1,000 a Nijar a shekarar 2023, fiye da 12,000 sun jikkata
Sabbin hotunan tauraron dan'adam sun gano alamun 'kaburburan bai-daya a El-Fasher a Sudan
MDD ta yi gargaɗin cewa yaƙin Sudan na gurgunta tattalin arzikin Sudan ta Kudu
Trump ya ce bai kamata Afirka ta Kudu ta kasance cikin G20 ba, ba zai je taronta a Johannesburg ba
'Yan Sudan sun ba da mummunan labarin yi wa mata fyade yayin da suke tserewa daga Al Fasher
An kashe mutane 40 a harin da aka kai wa taron jana'iza a yankin Kordofan na Sudan: MDD
Yadda biranen Afirka mafiya tsafta suke bayyana sauyin da ake samu a nahiyar
Sojojin Ruwa na Ghana sun kama ‘yan Nijeriya 10 da suka ɓuya a jirgin ruwan Panama a Tema
Harin jirgin sama maras matuƙi na RSF ya kashe mutane da dama a lardin Kordofan na Arewa a Sudan
Fiye da mutum 1,500 sun rasa matsugunansu a Sudan sakamakon taɓarɓarewar tsaro: MDD
Dakarun RSF sun kashe mata 300, sun yi wa 25 fyaɗe cikin awa 48 a Al Fasher – Minista
Amurka ta buƙaci a tattauna domin kawo ƙarshen yaƙin Sudan, ba amfani da ƙarfin soja ba
Ana fargabar dubban mutane na cikin 'mummunan hatsari' a birnin Al Fasher na Sudan da RSF ta ƙwace
Shugabar Tanzania Samia Hassan ta lashe zaɓen ƙasar da kashi 97.66 cikin 100
Tchiroma Bakary: Sojojin Kamaru sun yi wa jagoran 'yan adawar kasar rakiya zuwa wuri mai 'aminci'
Kudirin 1325 ya cika shekara 25: Me ya sa dole Afirka ta jagoranci samar da zaman lafiya a duniya
Dubban mutane sun tsere daga North Kordofan yayin da RSF ta zafafa kai hari a yankin Darfur na Sudan
Fararen-hula 177,000 sun maƙale a Al Fasher na Sudan, yayin da RSF ke ci gaba da kisa - Likitoci
Rundunar RSF ta amsa aikata 'take haƙƙi' a Al Fasher na Sudan
Kenya ta tabbatar da mutuwar mutum 11 'yan yawon bude ido a hatsarin jirgin da aka yi a kasar