| Hausa
KASUWANCI
2 MINTI KARATU
Kamfanin Olam ya karyata labarin badakalar biliyoyin kudade a Nijeriya
Jaridar Daily Nigerian da Prime Business Africa sun ruwaito labarin da ke cewa jami’an tsaro na sirri a Nijeriya sun bankado badakalar sama da dala biliyan 50 a rukunin kamfanin da ke Nijeriya.
Kamfanin Olam ya karyata labarin badakalar biliyoyin kudade a Nijeriya
Tambarin Ofishin kamfanin Olam da ke Singapore / Hoto: Reuters / Reuters
11 Satumba 2023

Kamfanin Olam na kasar Singapore (OLAG.SI), a ranar Litinin ya musanta rahotannin da aka watsa a kafafen yada labarai na Nijeriya a makon jiya, kan zargin cewa reshen kamfanin da ke kasar na da hannu a badakalar biliyoyin daloli.

Jaridar Daily Nigerian da Prime Business Africa sun ruwaito cewa jami’an tsaro na sirri a Nijeriya na binciken rukunin kamfanonin Olam a kasar da sauran sassan kamfanin da ke kasashen ketare da kuma wasu kamfanoni masu alaka da su kan badakalar sama da dala biliyan 50.

"Kamfanin ya musanta zarge-zargen rahotannin," a cewar wata sanarwa da ya fitar, kazalika Olman ya ba da umarni ga kwamitin bincikensa da ya sake yin nazari kan lamarin.

Hannun-jarin kamfanin ya fadi da kashi 7.8 cikin 100 kan farashin dala 1.180 da misalin karfe 06: 27 agogon GMT a ranar Litinin, bayan kasa da ya yi a watanni hudu na farkon shekarar nan kan dala 1.150.

Kazalika rahotannin sun yi zargin cewa akwai wasu 'yan Nijeriya da ke gudanar da ayyukansu a matsayin 'daraktoci na boge a kamfanonin'', sannan hukumomi sun gano wasu cibiyoyin hada-hadar kudade da ke da alaka da Olam.

An wallafa labarin rahoton ne a ranakun 7 da 9 na watan Satumba shekarar 2023.

Kamfanin Olam ya ce reshensa da ke Nijeria ya amsa bukatun karin bayani daga hukumomin Nijeriya kuma za su ci gaba da ba da hadin kai.

MAJIYA:TRT Afrika