Sabon shugaban ƙungiyar ƙawance ta ƙasashen yankin Sahel wato Mali da Burkina Faso da Nijar ya bayyana cewa bayan kaddamar da rundunar haɗin gwiwa ‘‘dole ne a samar da manyan ayyuka a kwanaki masu zuwa’’ a yankin da ke fama da ta’addanci.
Shugaban Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traore bai yi wani cikakken bayani ba a jawabinsa bayan da aka nada shi a matsayin sabon jagoran ƙungiyar ƙasashen Sahel (AES), wanda mambobinta uku da ke ƙarƙashin jagorancin mulkin sojoji suka fice daga ƙungiyar raya tattalin arzikin yankin yammacin Afirka wato ECOWAS a wannan shekarar.
An kafa ungiyar ƙawancen a shekarar 2023.
Mali, Burkina Faso da kuma Nijar su ne ƙasashen da suka fi shan wahala a yankin Sahel mai faɗi da ya zama wuri mafi muni a duniya wanda ya yi fice a ayyukan ta’addanci, inda ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai waɗanda ke da alaƙa da al’qaida da Daesh ke cin karensu ba babbaka.
Bayan kaddamar da rundunar haɗin gwiwa ta sojoji wadda ta kuduri aniyyar yaki da ƙungiyoyin ta’addanci, a wani taro da suka gudanar ranar Talata shugabannin ƙasashen sun amince su inganta tsaro da tattalin arzikin ƙasashensu.
Ƙungiyar ta "kawo ƙarshen dukkan rundunonin da suka mamaye ƙasashenmu," a cewar shugaban gwamnatin mulkin soji ta Nijar, Abdourahamane Tchiani, yana mai nuni da shawarar da ƙasashe AES suka yanke na korar Faransa da Amurka daga ƙasahensu.
"Babu wata ƙasa ko wata ƙungiya da za ta sake yanke shawara kan ƙasashenmu," a cewar Tchiani.
Ƙungiyar AES, wacce ta ƙunshi mutane miliyan 78, tana ci gaba da zurfafa haɗin kai a fannin tsaro, tattalin arziki da bayanai waɗanda ke nuna buƙatar samun 'yancin kai a yankin Sahel.















