Siyasar Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta ɗauki ɗumi sakamakon wasu bayanai da suka nuna cewa kowane lokaci daga yanzu Gwamna Abba Kabir Yusuf zai iya sauya sheka daga Jam’iyyar NNPP zuwa Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya.
Waɗannan rahotanni sun yi karfi ne a ƙarshen makon da ya gabata bayan wasu jiga-jigan ‘yansiyasa da makusantan gwamnan sun fito fili inda suka yi ta kiraye-kiraye a gare shi, da kuma uban gidansa na siyasa Rabiu Musa Kwankwaso cewa ya kamata su ja su zuwa Jam’iyyar ta APC.
Masu yin wannan kiran sun bayyana cewa shigar su jam’iyyar mai mulki zai kawo alfanu sosai ga zaman lafiya da ci-gaban jihar ta Kano.
Makusantan Gwamna Abba da ke kan gaba wurin wadannan kiraye-kiraye sun hada da babban jami’in tsare-tsare da karbar baki na gwamna, wato director of protocol Abdullahi Ibrahim Rogo da mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa da shugaban majalisar dokokin jihar ta Kano Jibril Ismail Falgore.

Waɗannan ‘yansiyasa da magoya bayansu daga yankunansu na Rogo da Dawakin Tofa sun gudanar da taron manema labarai a ƙarshen mako inda suka yi kira ga Sanata Rabiu Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir su ja su zuwa Jam’iyyar APC.
Hasali ma wasu rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yanmajalisar dokokin jihar ta Kano da dama da kuma ‘yan majalisar dokokin tarayya daga jihar sun bayyana aniyarsu ta shiga jam’iyyar APC, inda suke jira gwamnan ya jagorance su zuwa cikin jam’iyyar.
Sai dai wannan yiwuwar sauya sheƙa ya bijiro da batutuwa da dama sannan zai iya sauya lissafi da yawa a game da siyasar ta Kano.
Kana akwai manyan tambayoyi kamar: Shin Kwankwaso ne yake son tura Abba APC kafin ya bi shi daga bisani?
Ko dai Abba ne yake son yin gaban kansa ba tare da sahalewar uban gidansa ba?
Idan hakan ya faru, a iya cewa ya ci amanar mai gidan nasa?
Kuma idan ya shiga APC kuma jam’iyyar ta ba shi takara, shin Kwankwaso zai tsayar da wani dan takara a NNPP domin kawar da Abba?
Shin ma mece ce makomar Jam’iyyar NNPP, wadda Abba ne kadai gwamnanta a fadin Nijeriya?
Sannan mece ce makomar jiga-jigan ‘yan jam’iyyar APC na Jihar Kano, irin su tsohon gwamna Abdullahi Ganduje da mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau – wanda yake ta fafutukar ganin ya tsaya takarar gwamna a zabe mai zuwa - da tsohon dan takarar gwamnan jihar Nasiru Gawuna da mataimakinsa Murtala Sule Garo, idan Abba ya koma APC?
Tuni dai wasu bayanai suka nuna cewa da zarar gwamnan ya shiga APC, za a ajiye mataimakinsa Comrade Aminu Abdulsalam domin daukar Murtala Sule Garo domin su yi takara tare a zaben 2027.
Sai dai wasu na ganin hakan ma zai iya yamutsa hazo, ganin cewa akwai wadanda ake ganin sun fi shi cancanta da mukamin.
Masana harkokin siyasa na cewa shigar Abba jam’iyyar APC zai kawo karshen rigimar da ake yi a kan masarautar Kano, inda a halin yanzu ake da sarakuna biyu.
Kazalika ana gani hakan zai yayyafa ruwa a siyasar jihar, kasancewa gwamnan mutum ne mai saukin kai da ka iya tausasawa domin biyan bukatun mutane da dama.
Amma fa wasu na ganin muddin ya raba gari da Kwankwaso zai fadi babu nauyi domin kuwa shi ne ya dade yana kare shi daga mutanen da ake yi wa kallon kuraye a siyasar jihar Kano, wadanda ka iya cinye shi a siyasance.
Watakila babu wanda zai fi jin daɗi idan Gwamna Abba ya shiga APC kamar shugaban Nijeriya Bola Tinubu, domin kuwa hakan ka iya ba shi damar lashe jihar a zaɓen 2027 idan ya sake tsayawa takara.
A siyasar Nijeriya ba sabon abu ne sauya sheƙar masu mulki daga jam'iyyun da suka yi nasara a ƙarƙashinsu zuwa wasu jam'iyyun na daban, inda a baya bayan nan wasu gwamnonin jam'iyyun adawa suka koma jam'iyyar APC mai mulkin Nijeriya.


















