| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Harin ƙunar-baƙin-wake a wani Masallaci a Maiduguri ya kashe mutane da dama
Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan Jihar Borno Nahum Daso ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai ƙari da cewa mutum bakwai ne suka rasu.
Harin ƙunar-baƙin-wake a wani Masallaci a Maiduguri ya kashe mutane da dama
Tsawon shekaru jami'an tsaron Nijeriya na yaƙi da 'yanta'addar Boko Haram da ISWAP a arewa maso-gabashin kasar. Hoto: Reuters / Reuters
19 awanni baya

Wani bam da ake zargi ‘yan ƙunar-baƙin-wake sun dasa ya fashe a wani masallaci a birnin Maiduguri na Nijeriya kuma ya kashe mutane aƙalla bakwai a ranar Laraba, kamar yadda kamfanin labarai na AFP ya ambato wani shugaban ‘yanbindiga yana cewa.

Babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin wannan iƙirari da shugaban 'yanbindigar Babakura Kolo ya yi.

Sai dai kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wani ganau yana cewa sun fara da jin ƙara mai ƙarfin gaske, sannan baƙin hayaƙi ya turnuƙe masallacin da ke kasuwar Gamborou a Jihar a lokacin sallar Magariba.

Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan Jihar Borno Nahum Daso ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai ƙari da cewa mutum bakwai ne suka rasu.

Masu AlakaTRT Afrika - Boko Haram: Ana cin Borno da yaki, in ji Zulum

Amma wasu rahotanni sun ce mutane da dama ne suka mutu sakamakon harin.

An shafe shekaru ana fama da hare-haren 'yanta'addar Boko Haram a Maiduguri babban birnin Jihar Borno, duk da cewa birnin bai fuskanci wani babban hari ba tsawon shekaru.

'Yanta’adda sun sha kai hari a masallatai da wuraren da ke cike da jama'a a Maiduguri a hare-haren ƙunar-baƙin-wake da kuma abubuwan fashewa.

Boko Haram ta fara tayar da ƙayar baya a Jihar Borno a shekarar 2009, inda ta yi iƙirarin kafa "Daular Musulunci".

Duk da hare-haren soji da haɗin gwiwar dakarun MNJTF, hare-haren da ake kai wa lokaci-lokaci na ci gaba da barazana ga fararen-hula a arewa maso gabas.