Gwamnatin Ghana ta bayar da umarni mai ƙarfi da ya tuna wa ɗaukacin ministocin ƙasar cewa kada su bayyana duk wata muhimmiyar manufar gwamnati kafin majalisar minitoci ta ba da izinin yin hakan.
An bayar da umarnin ne a wata sanarwa da sakataren majalisar ministocin ƙasar Ghana, Farfesa Kwaku Danso-Boafo, ya sanya wa hannu.
Wannan ya biyo bayan abin da gwamnatin ƙasar ta bayyana a matsayin ɗabi’ar wasu ministoci ta bayar da sanarwa game da tsare-tsaren gwamnati “waɗanda suke iƙirarin cewa suna yi ne a madadin gwamnati” kafin majalisar ministoci ta gama tattatunawa a kansu.
Umarnin ya bayyana cewa irin wannan aikin ya saɓa wa tsarin mulki kuma dole ne sai majalisar ministoci ta amince da muhimman manufofi kafin a sanar da su ga ‘yan ƙasar.
“Majalisar ministoci tana son ta tuna wa dukkan ministoci cewa, bisa tsare-tsaren aikin gwamnati da kuma tsarin haɗa kai wajen yanke shawara da ke cikin kundin tsarin mulki, babu wata manufa ta gwamnati ko shiri da za a iya kira tsarin gwamnti sai har an miƙa shi ga Majalisar ministoci ta tattauna a kansa tare da amincewa da shi,” in ji sanarwar.










