Hukumar Kula da Zinari ta Ghana (GoldBod) ta ware kuɗi har cedi miliyan 35 domin farfaɗo da wani yanki na gandun dajin Tano Nimri da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba ta lalata, inda za a fara da gyaran hekta 50 na dajin.
Aikin, wanda ake gudanarwa tare da haɗin gwiwar Rundunar Sojin Ghana da Hukumar Kula da Gandun Daji, na da nufin dawo da ciyayi da bishiyoyi tare da farfaɗo da kusan hekta 200 na ƙasar da ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba suka lalata, in ji kamfanin dillancin labaran ƙasar Ghana (GNA).
A cewar wani rahoton binciken da GoldBod ta fitar da GNA ya ambato, injiniyoyin soji sun riga sun cike manyan ramukan haƙar ma’adinai guda 10, kuma suna kammala aikin daidaita ƙasa kafin miƙa wurin ga Hukumar Kula da Gandun Daji domin fara shuka bishiyoyi da sauran ayyukan farfaɗo da muhalli.
Aikin ya haɗa da kwashe ruwan da ya taru a ramukan da cike su da ƙasa da matse ƙasar da kuma daidaita wurin domin tabbatar da tsaron ƙasa da kuma samar da yanayin da zai dace da farfaɗo da muhalli.
Rahoton ya kiyasta cewa, an lalata hekta 192.4 na gandun dajin tsakanin shekarar 2021 da 2024.
Babban jami’in hukumar GoldBod, Sammy Gyamfi, ya ce wannan shiri ya nuna ƙudurin hukumar na tabbatar da amfani da albarkatun ƙasa cikin gaskiya da kuma kare muhalli, yana mai cewa ana sa ran faɗaɗa shirin farfaɗo da filayen da aka lalata a shekarar 2027.
An ware kusan cedi miliyan 27.9 domin ayyukan gyaran ƙasa, yayin da ake hasashen kashe cedi miliyan 7.2 wajen dasa bishiyoyi cikin shekaru 10.
A nasa ɓangaren, babban jami’in Hukumar Kula da Gandun Daji, Dakta Hugh Brown, ya ce aikin zai taimaka wajen kare halittu da kiyaye wuraren da ruwa ke taruwa da kuma tabbatar da ɗorewar albarkatun gandun daji.
A halin da ake ciki, Farfesa Ishmael Quaicoe, Daraktan Kula da Haƙar Ma’adinai Mai Inganci a Jami’ar Majalisar Ɗinkin Duniya, ya ce ana sa ran sake farfaɗo da wasu hekta 100 na gandun dajin da aka lalata a shekara mai zuwa.
Ana sa ran aikin gandun dajin Tano Nimri zai zama abin koyi wajen farfaɗo da sauran yankunan Ghana da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba ta lalata.






















