Gwamnatin Jihar Kano ta ɗauki sabbin jami’an tsaron dazuzzuka sama da 1,000 tare da tura su aiki a wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa tsaro da kuma kare al’ummomin da ke cikin haɗari a faɗin jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan a yayin bikin kammala horas da sabbin jami’an a ranar Asabar, 28 ga Nuwamba.
An ɗauki jami’an ne ƙarƙashin shirin kafa rundunar tsaron dazuzzuka ta ƙasa, wanda aka ƙaddamar ta ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA).
Jami’an suna aiki ne ƙarƙashin Hukumar Kula da Gandun Daji ta Ƙasa, kuma suna cikin babban shirin gwamnatin tarayya na ƙarfafa tsaro, musamman a yankunan dazuzzuka da ka iya zama mafakar masu aikata laifuka.
Gwamna Yusuf ya bayyana shirin a matsayin wani muhimmin mataki na tunkarar ƙalubalen tsaro, musamman ayyukan ’yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran laifukan da ke da alaƙa da dazuzzukan da ba su da cikakken iko ko kulawar hukumomi.
Ya ƙara da cewa ɗaukar ma’aikata da horas da jami’ai sama da 1,000 zai taimaka wajen inganta tattara bayanan sirri, sa ido da gudanar da ayyukan tsaro a al’ummomin da ke cikin dazuzzuka da sauran wurare masu rauni a faɗin Jihar Kano.
Gwamnan ya kuma yaba wa gwamnatin tarayya da ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro bisa ƙaddamar da shirin a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa tsarin tsaron ƙasar.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya samu wakilcin Sani Sani a wajen bikin. Wakilin ya isar da saƙon gwamnatin tarayya na ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen tsaro da nufin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Gwamna Yusuf ya buƙaci sabbin jami’an da su gudanar da ayyukansu cikin ƙwarewa, ladabi da kishin ƙasa, tare da mutunta haƙƙin ’yan ƙasa da kuma haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro.
Ya kuma tabbatar wa al’ummar Jihar Kano cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa duk wani ƙoƙari na tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da tsaro a faɗin jihar.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya sanya wa sanarwar hannu.














