| Hausa
NIJERIYA
4 minti karatu
Mata da ’yanmata a Gaza na cutuwa ta dindindin a fannin damar haihuwa - Rahoto
Rahoton ya kuma faɗaɗa binciken wani rahoton Amnesty da aka wallafa a watan Disamban 2024, wanda ya kammala da cewa Isra’ila ta aikata kisan kiyashi kan Falasɗinawa a yankin Gaza da aka killace.
Mata da ’yanmata a Gaza na cutuwa ta dindindin a fannin damar haihuwa - Rahoto
Palestinian women struggle to survive in Gaza / Anadolu Agency (Wire)
 

Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta fitar da wani cikakken rahoto da ke bayyana mummunar illar da ta ce kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza ya haifar ga mata da ’yanmata, tare da bayyana irin gwagwarmayar da suke yi ta yau da kullum domin rayuwa tun daga watan Oktoban 2023.

Rahoton, wanda aka fitar ranar Laraba mai taken “Babu yanayin da zai ba da damar rayuwa: Mata, ’yan mata da illolin jinsi na kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa Falasɗinawa a Gaza”, ya yi nazari kan yadda matakan Isra’ila ke shafar mata da ’yan mata daban da sauran al’umma.

Ya kuma faɗaɗa binciken wani rahoton Amnesty da aka wallafa a watan Disamban 2024, wanda ya kammala da cewa Isra’ila ta aikata kisan kiyashi kan Falasɗinawa a yankin Gaza da aka killace.

Rahoton ya ce: “Ayyukan Isra’ila a Gaza tun daga ranar 7 ga Oktoban 2023 sun yi mummunar illa ga rayuwar mata da ’yan mata.

Sojojin Isra’ila sun kashe dubban mata da ’yanmata, inda matsakaicin adadin ya kai kusan 30 a kowace rana kafin yarjejeniyar tsagaita wuta.”

Ya bayyana cewa yawancin mace-macen sun faru ne sakamakon hare-haren da suka saɓa wa dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa.

Ya ƙara da cewa killace yankin da Isra’ila ta yi ya jawo mutuwar wasu mata da ’yan mata da ba a san adadinsu ba.

Rahoton ya ce: “An tilasta wa mata da ’yan mata shiga gwagwarmayar neman tsira ta yau da kullum, wadda ke cike da baƙin ciki, raunin tunani, cin zarafi, sake raba su da matsugunansu akai-akai, matsanancin ƙarancin abubuwan buƙata, tsoro da kuma babban rashi.”

Ya ƙara da cewa an hana mata da ’yan mata samun muhimman ayyukan kiwon lafiya, ciki har da na lafiyar jima'i da haihuwa, yayin da suke fuskantar ƙarin barazanar cin zarafi bisa jinsi.

Rahoton ya jaddada cewa: “Matakan Isra’ila sun kuma tauye ikon Falasɗinawa na yanke shawara kan ko za su haifi ’ya’ya da kuma lokacin da za su yi hakan, ɗaukar ciki, kammala cikin lafiya da kuma haihuwa cikin aminci.”

Ya bayyana cewa mata da ’yan mata a Gaza sun fuskanci waɗannan illoli akai-akai kuma a jere, lamarin da ya haifar musu da mummunar illa ta fuskar lafiyar jiki, tunani da haihuwa.

Ya kuma ce: “Rashin biyan buƙatun mata na lafiyar haihuwa, nauyin kula da iyali da ya rataya a wuyansu saboda jinsi, da kuma rashin daidaiton da suka daɗe suna fuskanta, duk sun ƙara tsananta illolin da suka sha.

“Waɗannan take haƙƙoƙi sun kasance wani muhimmin ɓangare na kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa Falasɗinawa a Gaza.”

Rahoton ya sake jaddada cewa akwai shaidun da ke nuna cewa kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa Falasɗinawa a Gaza ya ci gaba duk da yarjejeniyar tsagaita wuta ta Oktoban 2025.

Hakan ya haɗa da ci gaba da ƙaddamar da yanayin rayuwa da aka tsara da gangan domin haifar da hallaka Falasɗinawa a yankin.

Ya kuma ce Isra’ila ta ɗauki matakan da suka hana haihuwa tsakanin Falasɗinawa a Gaza, yana mai bayyana hakan a matsayin wani ƙarin aikin da aka haramta ƙarƙashin sashe na II(d) na Yarjejeniyar Yaƙi da Kisan Kiyashi, idan aka aikata shi da niyyar da dokar ta tanada.

An gudanar da binciken ne bisa dogayen hirarraki 228 da aka yi ta kafafen sadarwa daga ranar 7 ga Oktoban 2023 zuwa 1 ga Oktoban 2026.

Waɗanda aka yi wa tambayoyin sun haɗa da mata da ’yanmata, shaidu, ma’aikatan kiwon lafiya da kuma ma’aikatan ƙungiyoyi masu zaman kansu da hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya.

Rahoton ya tattara bayanai kan yawan kashe-kashe da raunata mutane, haɗarin da mata ke fuskanta wajen samun kulawar lafiya lokacin ciki da haihuwa, rushewar ayyukan kula da lafiyar mata masu juna biyu, tilasta wa mutane barin matsugunansu, tauye ’yancin mata na yanke shawara kan haihuwa, tsare mutane bisa jinsi da sauran illoli.

Amnesty International ta kuma yi kira ga Isra’ila da ta kawo ƙarshen dukkan take haƙƙoƙin Falasɗinawa a Gaza nan take, ta kare ayyukan kiwon lafiyar jima'i da haihuwa da haƙƙoƙin da suka shafe su, ta kawo ƙarshen cin zarafi bisa jinsi da tsare mutane ba bisa ƙa'ida ba, tare da tabbatar da haɗa iyalan da aka raba.

Ƙungiyar ta kuma buƙaci sauran ƙasashe su yi amfani da dukkan hanyoyin siyasa da diflomasiyya da suke da su domin tabbatar da cewa Isra’ila ta cika nauyin da dokokin ƙasa da ƙasa suka ɗora mata.

Hakan ya haɗa da ɗaukar matakan hana kisan kiyashi da hukunta masu aikata shi, tare da guje wa duk wani abu da zai taimaka wajen aikata take haƙƙoƙi.