| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
'Yanbindiga sun kashe mutum bakwai a wani sabon harin da suka kai Jihar Neja
Rundunonin sojin sama da na ƙasa na Nijeriya sun daƙile wani harin da wasu 'yanbindiga suka kai wani ƙauye a jihar Neja a wannan makon, inda suka kashe mutane bakwai, kamar yadda 'yansanda da ma'aikatan agaji suka bayyana a ranar Asabar.
'Yanbindiga sun kashe mutum bakwai a wani sabon harin da suka kai Jihar Neja
Wata ƙungiyar agaji ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mutane bakwai ne suka mutu a harin, ciki har da wata mata da 'ya'yanta. / Reuters (Wire)
 

Rundunonin sojin sama da na ƙasa na Nijeriya sun daƙile wani harin da wasu 'yanbindiga suka kai wani ƙauye a jihar Neja a wannan makon, inda suka kashe mutane bakwai, kamar yadda 'yansanda da ma'aikatan agaji suka bayyana a ranar Asabar.

Wani mai magana da yawun rundunar 'yansandan Jihar Neja ya ce wasu da ake zargin 'yanbindiga ne sun kai hari ƙauyen Lumma-Sanke a daren ranar Juma'a.

Harin ya zo ne kwanaki kaɗan bayan wasu hare-hare na ramuwar gayya da aka kai kan ƙauyukan da ke maƙwabtaka da juna, inda rahotanni suka ce an kashe mutane fiye da 80.

“Harin ya jefa mazauna yankin cikin firgici, inda suka tsere daga gidajensu domin tsira da rayukansu, yayin da maharan suka cinna wa mafi yawan gidajen wuta,” in ji mai magana da yawun ‘yansandan.

 “A yayin harin, ɓangaren rundunar sojin sama ya kai ɗauki, inda ya bayar da tallafin hare-haren sama ga dakarun ƙasa. Dakarun biyu sun haɗa kai wajen fatattakar 'yanbindigar, waɗanda suka tsere daga yankin,” kamar yadda ya ƙara da cewa.

Wata ƙungiyar agaji ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mutane bakwai ne suka mutu a harin, ciki har da wata mata da 'ya'yanta.

Ƙauyen Lumma-Sanke yana kusa da Luman Ba'are, wanda ƙauye ne da al'ummar Kambari ke zaune, wanda wasu da ake zargin makiyaya ne suka kai wa hari makon da ya gabata, inda suka kashe mutane 11.

Bayan wannan hari, wasu 'yan sa-kai na ƙabilar Kambari sun kai hare-haren ramuwar gayya kan ƙauyukan Fulani da ke maƙwabtaka da su, wato Wawa da Gada Oli, inda hukumomi suka ce an kashe kusan mutane 70.

Dubban mutane ne suka rasa rayukansu a irin waɗannan rikice-rikice, waɗanda galibi ke faruwa tsakanin al'ummomin ƙabilu daban-daban, sakamakon ayyukan ƙungiyoyin masu aikata laifuka da ke satar mutane tare da satar shanu.