| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Jose Mourinho ya ce ya tsani a ringa kwatanta Jude Bellingham da Zinedine Zidane
Duk da cewa har yanzu shekarun Bellingham 23 kacal, tuni matashin ya nuna bajinta musamman bayan zuwansa Real Madrid, inda ko a kakar bana ya ci ƙwallaye 7 cikin wasanni 18 da ya buga.
Jose Mourinho ya ce ya tsani a ringa kwatanta Jude Bellingham da Zinedine Zidane
Jude Bellingham na tashen tagomashi ƙarƙashin koci Jose Mounrinho / AP (Wire)
 

Kocin Real Madrid, Jose Mourinho ya yi watsi da masu ƙoƙarin kwatanta ɗanwasan Madrid, Jude Bellingham, da toshon ɗanwasan ƙungiyar, Zinedine Zidane.

Wannan na zuwa ne yayin da Bellingham ke tashe ƙarƙashin Mourinho, musamman a wasan da Madrid ta doke PSV a wasan gasar Zakarun Turai ta farkon makon nan.

Matashin ɗanwasan ɗan Ingila, ya nuna bajinta wajen zura ƙwallo ɗaya cikin 5 da Madrid ta ci, da tallafin ƙwallo ɗaya, inda aka tashi wasan suna da nasarar ci 5-1.

Yayin wani taron manema labarai gabanin wasan da zai jagoranta ranar Asabar, 28 ga Nuwamba tare da Alaves, Mourinho ya soki yadda ake da zuzuta tasirin Bellingham a aikinsa na ɗanwasan tsakiya.

Mourinho ya nesanta kansa daga masu wannan muhawar don tantance wa ya fi zarra tsakanin Bellingham da Zidane, wanda tauraron Faransa ne da kuma ya taɓa horar da Real Madrid.

Da aka tambaye shi game da ‘yanwasan biyu, Mourinho ya ce, "Zidane na cikin mafi kyawun ‘yankwallon zamaninsa; shi ma Jude [Bellingham] tuni ya shiga cikin mafi kyawun ‘yankwallon zamaninsa."

Amsar Bellingham

Mourinho ya zaɓi ƙin kwatanta ƙwarewar ‘yanwasan biyu, yana mai cewa kowa gwani ne a zamaninsa. Kuma abin da ya kamata shi ne a kwatanta kowanne daidai da zamaninsa.

Duk da cewa har yanzu shekarun Bellingham 23 kacal, tuni matashin ya nuna bajinta musamman bayan zuwansa Real Madrid, inda ko a kakar bana ya ci ƙwallaye 7 cikin wasanni 18 da ya buga.

Sai dai ko shi kansa Bellingham da aka taɓa tambayar sa ko yana kallon kansa daidai da matsayin Zidane, matashin ya ce Zidane yana da “fifiko matuƙa” sama da shi.

A yanzu dai Bellingham da kocinsa Mourinho sun mayar da hankali kan wasansu na gasar La Liga da za su kara da Deportivo Alaves a gida Santiago Bernabeu.

A halin yanzu Real Madrid tana matsayi na biyu a teburin babbar gasar ta Sifaniya, da maki 33 cikin wasanni 13. Wato suna ƙasan Barcelona da tazarar maki 3.