Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Nijeriya NCoS, ta ce akwai fursunoni fiye da 4,000 da aka yanke wa hukuncin kisa a fadin kasar, inda wasu daga cikinsu suka shafe fiye da shekaru 10 suna jiran a zartar musu da hukuncin.
Babban kwanturolan hukumar, Sylvester Nwakuche, ne ya bayyana hakan a birnin Ilorin da ke Jihar Kwara, yayin ziyarar da ya kai gidan yarin Oke-Kura bisa umarnin Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Ojo.
Ziyarar tasa ta biyo bayan rahotannin mutuwar wasu fursunoni uku da aka yanke wa hukuncin kisa a gidan yarin, lamarin da ake zargin ya faru a cikin yanayi mai cike da shakku.
Nwakuche ya bukaci gwamnonin jihohi da su yi amfani da ikon da doka ta ba su, ta hanyar sauya hukuncin kisan da aka yanke wa fursunonin zuwa daurin rai-da-rai ko kuma sanya hannu domin a zartar musu da hukuncin kisa.
Ya ce jinkirin yanke hukunci kan makomar fursunonin da aka yanke wa hukuncin kisa na daga cikin abubuwan da ke haddasa cunkoso a gidajen yari a faɗin kasar.
A cewarsa, akwai fursunoni fiye da 70 da aka yanke wa hukuncin kisa a gidan yarin Oke-Kura, inda wasu daga cikinsu suka shafe fiye da shekaru 10 suna jiran a zartar musu da hukuncin.
Ya kuma bayyana cewa gidan yarin, wanda Turawan mulkin mallaka suka gina, yana ɗauke da fursunoni kusan 685, duk da cewa ba a tsara shi domin ɗaukar adadi mai yawa haka ba.
Babban jami'in ya ce cunkoson na ƙara matsin lamba ga jami'an gidan yari da kayan amfani na gidajen, tare da kawo cikas ga tsarin rarraba fursunoni da kuma shirye-shiryen horas da su sana'o'i domin gyara halayensu.
Ya kara da cewa hukumar ta fara tattaunawa da gwamnatocin jihohi, inda take neman su yi la'akari da sauya hukuncin kisa zuwa ɗaurin rai-da-rai ga wasu fursunoni.
Nwakuche ya ce hakan zai ba da damar mayar da fursunonin zuwa wasu gidajen yari da ba su da cunkoso, inda za su samu horon sana'o'i da shirye-shiryen gyaran hali domin su zama masu amfani ga al'umma bayan sun kammala zaman gidan yari.















