| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
Rasha ta harbo daruruwan jirage marasa matuka a kusa da Moscow a dare daya
Magajin garin Moscow ya ce fiye da jirage marasa matuka 460 ne suka doshi yankin tsakanin daren Juma'a zuwa safiyar Asabar inda suka harbo mafi yawancinsu tun kafin su isa Moscow, yayin da suka lalata wasu 123 a lokacin da suke dab da shiga Moscow.
Rasha ta harbo daruruwan jirage marasa matuka a kusa da Moscow a dare daya
Wani jirgi mara matuƙi mai kai hari mai kafaffun fuka-fuki na Yukren yana tashi a ranar 11 ga Nuwamba, 2026. / AFP Archive
 

Rasha ta ce na'urorin tsaron sararin samaniyarta sun kakkabo daruruwan jirage marasa matuka da suka nufi yankin Moscow cikin dare.

Magajin garin Moscow, Sergei Sobyanin, a wani sako da ya wallafa a dandalin sada zumunta na Max, mai samun goyon bayan gwamnatin Rasha, ya bayyana cewa fiye da jirage marasa matuka 460 ne suka doshi yankin tsakanin daren Juma'a zuwa safiyar Asabar.

Ya ce dakarun tsaron sararin samaniyar Rasha sun kakkabo mafi yawancinsu tun kafin su isa Moscow, yayin da suka lalata wasu 123 a lokacin da suke dab da shiga babban birnin kasar.

Gargaɗi da martani

A ranar Alhamis, shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya yi gargadi a karo na biyu cikin mako guda cewa Rasha na shirin kaddamar da gagarumin hari kan Ukraine.

A cikin wani sakon bidiyo da ya gabatar da daddare ya ce: “Abin takaici, muna da bayanan sirri da ke nuna cewa Rasha na shirin sake kaddamar da wani gagarumin hari.”

Zelenskyy ya ce yana jiran rahoto daga ma'aikatar harkokin wajen kasarsa kan tattaunawar da take yi da kawayenta domin samar wa Ukraine karin makaman kare sararin samaniya.

A nasa bangaren, shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana a ranar Alhamis cewa ya bukaci Shugaban Rasha, Vladimir Putin, da ya dakatar da dukkanin ayyukan ta'addancin soji da yake yi wa kasashen Turai, a lokacin ganawarsu da suka yi a kasar China a makon da ya gabata.

Trump, wanda ya bayyana Putin a matsayin abokinsa, ya ce yana ganin bukatar tasa za ta iya taimakawa wajen cim ma yarjejeniyar kawo karshen yakin.

Shi ma wakilin Amurka, Jared Kushner, ya yi gargadin cewa bai kamata rikicin ya kara kamari ba, inda ya bayyana yakin a matsayin wani “yaƙi na bayan fage, inda Turai ke ɗaukar nauyin Ukraine da makamai da kudade domin yakar Rasha.”

A cikin 'yan watannin nan, Rasha da Ukraine sun kara yawan hare-haren jirage marasa matuka da sauran makamai yayin da yakin ke ci gaba da shiga shekararsa ta biyar.