| Hausa
TURKIYYA
2 MINTI KARATU
Turkiyya da Masar za su kara yawan jiragen sama da ke safara tsakaninsu
Turkiyya da Masar sun sanya hannu kan yarjejeniyar ninka yawan jiragen da suke safara tsakanin kasashen biyu.
Turkiyya da Masar za su kara yawan jiragen sama da ke safara tsakaninsu
A  karkashin sabuwar yarjejeniyar, jiragen saman da ke kai komo tsakanin Turkiyya da Masar su 30 za su karu zuwa 67 a cikin mako guda. / Photo: AA / Others
5 Satumba 2024

Adadin jiragen saman da ke kai-komo tsakanin Turkiyya da Masar za su karu sama da ninki guda, in ji Ministan Sufuri da Gina Ƙasa na Turkiyya a ranar Alhamis.

A karkashin sabuwar yarjejeniyar, jiragen saman da ke kai komo tsakanin Turkiyya da Masar za su karu daga 30 zuwa 67 a cikin mako guda, in ji sanarwa ta Abdulkadir Uraloglu.

A gawanar da aka yi a ranar Laraba a yayin Taron Hadin Kai na Kasashen Biyu a babban birnin Ankara na Turkiyya karkashin shugabancin Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da takwaransa na Masar Abdel Fattah el Sisi, an sanya hannu kan yarjeniyoyi a bangarorin sufurin jirgin kasa, da fasahar sadarwa da sufurin jiragen sama.

Wannan ne karo na farko da shugaban kasa daga Masar ya ziyarci Turkiyya a cikin shekaru sama da 10, yunkurin wani bangare na Turkiyya na inganta alakarta da makotanta da ke gabar tekun Bahar Rum.

MAJIYA:TRT Afrika