'Yan ci-rani huɗu sun mutu bayan jiragen ruwa guda biyu da ke ɗauke da kusan mutane 100 sun kife a kusa da gaɓar ruwan Al-Khums a arewa maso yammacin Libya, in ji ƙungiyar bayar da agaji ta Libyan Red Crescent.
Ƙungiyar ta ce ta samu rahoto daga daren Alhamis game da jiragen ruwan 'yan gudun hijira guda biyu da suka kife a bakin ruwa a Al-Khums.
Jirgin farko yana ɗauke da 'yan ci-rani 26 daga Bangladesh, inda aka samu huɗu daga cikinsu matattu.
Jirgin na biyu yana ɗauke da mutane 69, ciki har da ‘yan Masar biyu da 'yan Sudan 67, da yara takwas, in ji ƙungiyar ta Red Crescent.
Hukumar ta kara da cewa an tura ma’aikatan agajin gaggawa zuwa wurin don ceto waɗanda suka tsira da ɗauko gawawwakin waɗanda suka mutu, da kuma ba da kulawa.
Ana ganin Libya a matsayin wuri ficewa ga masu son tafiya ci-rani cikin sauƙi ba tare da izini ba da ke ƙoƙarin isa Turai ta haramtacciyar hanya ta hanyar amfani da teku.
Hukumomi na ci gaba da fuskantar ƙaruwar ƙalubalen 'yan ci-rani, yayin da ƙasashen Tarayyar Turai dake bakin Tekun Bahar Rum ke nuna damuwa game da yawan zirga-zirgar 'yan gudun hijira marasa izini zuwa bakin tekunsu.
Kungiyar Kula da ‘Yan Ci-rani ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM) a ranar Laraba ta ce adadin 'yan gudun hijirar da suka mutu yayin ƙoƙarin ketare tsakiyar Tekun Bahar Rum a wannan shekara ya riga ya wuce 1,000.

















