Rundunar tsaro ta farin kaya wadda aka fi sani da DSS a Nijeriya ta gurfanar da mutum bakwai a gaban wata babbar kotun Tarayya a Birnin Kebbi bisa zargin hannu a ta’addanci da garkuwa da mutane da mallakar bindigogi ba bisa ƙa’ida ba.
An gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban maishari'a Emmanuel Gakko, a cikin ƙararraki uku da DSS ta shigar a Jihar Kebbi, a arewa maso yammacin Nijeirya.
A ƙarar ta farko, mai lamba FHC/KB/CR/58/2026, waɗanda ake ƙara biyar — Garba Safiyanu da Lawali Adamu da Abubakar Murtala da Kabiru Sani da Salah Muhammad — suna gaban kotun ne bisa tuhuma uku da suka shafi haɗa bakin don aikata laifi da ba da tallafi ga wata ƙungiyar ta’addanci da kuma ƙin ba da bayanai game da harkokin ta’addanci.
Masu gabatar da ƙara sun yi zargin cewa waɗanda ake tuhumar sun sayi tare da sayar da dabbobi da mambobin ƙungiyar Lakurawa da ke aika-aika a sassan ƙananan hukumomin Argungu da Augie a Jihar Kebbi suka sato.
Sun ce abin waɗanda ake zargi suka aikata ya kasance ba da tallafi na kaya ga ƙungiyar da kuma ɓoye bayanai game da harkokin ƙungiyar.

An yi zargin cewa an aikata laifukan ne ranar 20 ga watan Mayun 2026, a ƙaramar hukumar Argungu.
A ƙara na biyu, mai lamba FHC/KB/CR/59/2026, an tuhumi Bello Abdullahi, wanda aka sani da suna Riskuwa, da laifin ɓoye bayanai game da ta’adancin da tallafa wa ta’addanci da kuma taimaka wa harkokin su.
Masu gabatar da ƙaran sun ce Abdullahi ya ɓoye bayanai game da harkokin wani da ake zargin shugaban ‘yan ta’adda ne mai suna Abdullahi, wanda aka ce ɗan uwansa ne da kuma mambobin ƙungiyarsa bayan wani hari kan ƙauyen Cikanwa a ƙaramar hukumar Danko-Wasagu.
An kuma zarge shi da magana da wanda ake zargin shi ne shugaban ‘yanta’addan ta waya da kuma ba da bayanai game da harkokin ƙungiyar.
Masu gabatar da ƙaran sun kuma yi zargin cewa tattaunawarsu ta haɗa da kashe Nadajo Bakumi yayin wani harin da suka kai daga farko a kan ƙauyen.
An kuma zargi Abdullahi da bayyana yarda ya tuntuɓi ‘yan uwan sauran waɗanda ƙungiyar ta yi garkuwa da su don cinikin biyan kudin fansa.
Laifukan da ake zargin ya aikata ya faru ne ranar 4 ga watan janairun 2026, a garin Maga, a ƙaramar hukumar Danko-Wasagu.
Lamarin na uku ya shafi Kyale Ayuba, wanda aka fi sani da suna Jikan Dole, wanda aka tuhuma da mallakar bindiga ba bisa ƙa’ida ba.
Masu gabatar sun yi zargin cewa an sami Ayuba da ƙaramar bindigar da ake era a gida da gidan harsasai da harsasai biyar masu girman milimita 9, abin da ya saɓa wa sashe 27(1)(a) na dokar bindigogi.
Abdullahi Shehu, daraktan harkokin shari’a a DSS, ne ya gabatar da ƙarar a madadain gwmanatin Tarayyar Nijeriya.
Hamza Nagari ya wakilci huɗu daga cikin waɗanda ake zargi a shari’ar, yayin da Sadiq Shehu ya fito a madadin na biyar daga cikin waɗanda ake zargin . S. M. Danyaro ya wakilci Bello Abdullahi a shari’a na biyun.
Dukkan waɗanda ake zargi bakwai ɗin sun ce ba su yi laifi ba bayan an karanta musu tuhume-tuhumen.
Gakko ya ɗaga saurarar ƙararrakin uku zuwa ranar 3 ga watan Disamban 2026.














