Shugabar ƙasar Tanzaniya, Samia Suluhu Hassan, ta samu nasarar lashe zaɓe da rinjaye mai yawa, kamar yadda sakamakon da aka fitar a hukumance ya nuna a ranar Asabar, bayan da aka tsare ko kuma aka hana wasu muhimman 'yan takara shiga zaɓen da ya haifar da zanga-zanga da ka tashin hankali na tsawon kwanaki.
Sakamakon ƙarshe ya nuna cewa Hassan ta samu kashi 97.66 cikin ɗari na ƙuri'un zaɓe, inda ta yi nasara a kowanne yanki, kamar yadda hukumar zaɓe ta sanar a gidan talabijin na gwamnati. An bayyana cewa za a gudanar da bikin rantsar da ita cikin gaggawa a ranar Asabar, kamar yadda gidan talabijin na gwamnati ya sanar.
Babbar jam'iyyar adawa, Chadema, ta bayyana cewa ɗaruruwan mutane sun rasa rayukansu a hannun jami'an tsaro tun bayan da zanga-zanga ta ɓarke a ranar Laraba da aka yi zaɓen yayin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta nuna damuwa kan “rahotannin mutuwa da raunuka.”
Kakakin Chadema ya shaida wa AFP cewa kimanin mutum 700 ne suka mutu, yana mai dogaro da bayanai daga asibitoci da cibiyoyin lafiya. Wani jami'in tsaro da wani jakada a Dar es Salaam su ma sun ce adadin mutanen da suka mutu ya sai dai a yi batun “daruruwa.”
An katse intanet, an saka dokar hana fita a duk faɗin ƙasa
Hukumomi sun katse intanet, sun saka dokar hana fita a duk faɗin ƙasa, tare da taƙaita aikin 'yan jarida, wanda hakan ya sa ya zama da wahala a tabbatar da gaskiyar abubuwan da ke faruwa.
Gwamnatin Hassan ta musanta amfani da “ƙarfin da ya wuce kima,” inda Ministan Harkokin Waje, Mahmoud Thabit Kombo, ya shaida wa Al Jazeera cewa babu “adadi” na mutanen da suka mutu.
Kungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun ce zaɓen ya kasance cike da tsoratarwa da kuma sace-sacen shugabannin adawa a kwanakin da suka gabata kafin zaɓen. An hana Chadema shiga zaɓen, kuma shugabansu yana ci gaba da fuskantar shari'a kan zargin cin amanar ƙasa.
Yawancin fushin jama'a ya karkata kan ɗan Shugabar ƙasa, Abdul Halim Hafidh Ameir, wanda masu suka ke zargi da shirya matakan murƙushe masu adawa.
Masana sun ce Hassan, wadda ta karɓi mulki a shekarar 2021 bayan rasuwar wanda ya gabace ta John Magufuli, ta yi ƙoƙarin ƙarfafa ikon ta a cikin jam'iyyarta da kuma kawar da masu adawa daga cikin gida.
Shugaban sojoji, Jacob Mkunda, a ranar Alhamis ya bayyana masu zanga-zangar a matsayin “'yan ta'adda” tare da yin alkawarin bayar da goyon baya ga shugabar ƙasa.










