| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
ECOWAS ta ayyana dokar ta-ɓaci a Yammacin Afirka kan 'rashin zaman lafiya' na siyasa da tsaro
Sanarwar ECOWAS na zuwa ne bayan yunƙurin juyin mulki da sojoji suka yi a ƙarshen makon jiya a Jamhuriyar Benin, wanda ya biyo bayan wani juyin mulkin da aka yi a Guinea-Bissau.
ECOWAS ta ayyana dokar ta-ɓaci a Yammacin Afirka kan 'rashin zaman lafiya' na siyasa da tsaro
ECOWAS ta nuna damuwa a kan abin da ta kira "rashin zaman lafiya" na siyasa da tsaro a Yammacin Afirka. / AP
10 Disamba 2025

.mƘungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta ayyana dokar ta-ɓaci bayan “rashin zaman lafiya” na siyasa da tsaro ya girgiza yankin, kamar yadda kafofin watsa labarai suka ruwaito a Nijeriya.

"Abubuwan da suka faru cikin ‘yan makonnin nan sun nuna muhimmancin sake tunani mai zurfi game da makomar dimokuraɗiyyarmu da kuma buƙata ta gaggawa ta tsaron al’ummominmu," in ji shugaban hukumar ƙungiyar ECOWAS Oumar Touray wanda ya bayyana haka a Abuja.

Sanarwar na zuwa ne bayan yunƙurin juyin mulki da sojoji suka yi a ƙarshen makon jiya a Jamhuriyar Benin, wanda ya biyo bayan wani juyin mulkin da aka yi a Guinea-Bissau.

Masu AlakaTRT Afrika - Shugaba Tinubu ya jinjina wa sojojin Nijeriya kan daƙile juyin mulki a Benin

Touray ya ce zaɓuka sun zama wani "muhimmin abin da ke janyo rashin zaman lafiya a al’ummarmu."

Rashin tsaro

Baya ga sabbin matakan soji, ya yi ishara ga wasu muhimman haɗɗura, ciki har da rashin mutunta tsare-tsaren sauya gwamnati da rashin baiwa kowa damar shiga a dama da shi a siyasa da kuma ƙarin tasirin ƙungiyoyin ‘yan ta’adda da masu aikata laifuka da matsin lamba kan diflomasiyya da haɗin kai na ƙasashe mambobin ECOWAS.

Da yake kira da a ƙara yawan tattaunawa, Touray ya yi kira ga ECOWAS ta "haɗa kayayyakin aikinmu domin tunkarar barazanar ta’addanci da ‘yanbindiga da suke aika-aika ba tare da martaba kan iyakoki ba."