| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Aƙalla mutum 81 sun mutu cikin makonni sakamakon ambaliyar ruwa a Kenya
Wurare da yawa a Kenya sun sha fama da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a cikin 'yan makonnin nan, inda babban birnin ƙasar Nairobi ya fi fama da matsalar.
Aƙalla mutum 81 sun mutu cikin makonni sakamakon ambaliyar ruwa a Kenya
Ambaliyar Kenya ruwa na ƙaruwa sosai a farkon watan Maris Musamman a Nairobi. / AP / AP
23 Maris 2026

Ruwan saman da guguwa da suka haddasa ambaliyar ruwa a Kenya sun kashe aƙalla mutum 81 a cikin wannan watan, kamar yadda hukumomi suka bayyana ranar Lahadi, yayin da ruwa ya ci gaba da ɓarna a sassan ƙasar.

A yankin yammacin ƙasar da ruwan ya fi zuba, mazauna suna wucewa cikin ruwan ambaliya yayin da kayayyakinsu ke kulle a kansu kuma suke ƙaurace wa cikin kwale-kwale da suka cika sosai.

Ambaliya da ke haɗuwa cikin sauri ta shanye ƙauyuka gabaɗaya a jihar Kisumu, inda ta lalata kimanin kidada 1,200 (3,000 acres) na gonaki, kuma ya share amfanin gona.

Fiye da iyalai 3,000 lamarin ya tilasta wa barin gidajensu a garin Nyakach, inda wasu suke fakewa a sansanonin kuɓutarwa takwas, in ji mazauna wurin, yayin da tashin ruwa daga Kogin Mirui da ya cika yake zubewa ke barazana a garin.

"Mun rasa gonaki da yawa da zaizayar ƙasa mai yawa da ababen da muka shuka," in ji Sarkin Nyakach, Seth Oluoch Agwanda, mai shekara 57.

Ta’adi mai yawa

Mafi yawan waɗanda suka mutu a babban birnin ƙasar Nairobi ne, inda ya mutum 37 suka rasa rayukansu, in ji hukumomi.

"Abin taƙaicin shi ne jumullar adadin waɗanda lamarin ya kashe ya kai ga 81," in ji mai magana da yawun rundunar ‘yansandan ƙasar Muchiri Nyaga a wata sanarwa.

"Bugu da ƙari, ambaliyar ruwa ta shafe wurare da yawa inda ya raba kimanin iyalai 2,690 da gidajensu da kuma haddasa lalata ababen more rayuwa da kuma kadarori."

A ranar Jumma’a da dare, hukumomi sun yi kira ga mazauna su ƙaurace daga wasu unguwannin marasa galihu da ke ƙasa-ƙasa daga dam ɗin Nairobi, suna masu gargaɗi ga barazanar ambaliya da ke kusa yayin da ƙaruwar matakin ruwa ke barazanar karya ginshiƙin da aka yi wa dam ɗin, in ji kafafe watsa labaran cikin ƙasar.

Kawo yanzu dai dam ɗin yana nan. An yi hasashen cewa ruwan saman zai ci gaba da zuba zuwa ranar Talata.

Hukumomin sun yi kira da "a mayar da hankali sosai".

Mutum biyu sun nuste a ruwa cikin daren ambaliya a garin Kiambu, a wajen babban birnin ƙasar, kamar yadda ‘yan sanda suka shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP.

Sauyin yanayi

Mutum biyu sun kuma mutu yayin da ruftawar ƙasa ya daki ƙauyen Kasaka da ke yammacin ƙasar, lamarin da ya bunne gidaje masu yawa, kamar yadda kafa mai zaman kanta ta Citizen TV ta ruwaito.

Ruwan saman na watan Maris ya mayar da titunan Nairabo koguna masu ƙarfi, inda suke janyo ambaliya a dubban gidaje da kamfanoni.

A Nyakach, da ke yammaci, ƙananan yara suna tafiya cikin ruwan da ya kai gwiwa kuma mazauna suna tsiyaye ruwa daga gidaje da ruwa kwarara ciki, duk da cewa wasu gidajen sun nutse har kan kwano.

"Muna ƙauracewa domin wurin da muke zaune ya yi ambaliya sosai. Har yanzu ba mu san inda za mu tafi ba domin samun mafaka da dabbobinmu domin babu wani gida da a yi ambaliya ba," kamar yadda Kennedy Oguta, mai shekara 50, ya shaida wa AFP.

Masana kimiyya sun ce sauyin yanayi da ayyukan ɗan’adam ke janyowa yana ƙara yiwuwa da tsawo da kuma tsananin matsalolin yanayi.

Bincike sun nuna cewa gabashin Afirka ya yi fama da ruwan sama da yawa da fari cikin fiye da shekaru ashirin da suka gabata.