| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
7 minti karatu
Iran ta kai hari kan maƙwabtanta a gaɓar teku, ta ƙara daƙile jigilar mai yayin da fargaba ke ƙaruwa
Tashin farashin mai da kuma katse tafiyar tankokin mai na ƙara matsi a kan Washington yayin da rikicin ke yaɗuwa a yankin.
Iran ta kai hari kan maƙwabtanta a gaɓar teku, ta ƙara daƙile jigilar mai yayin da fargaba ke ƙaruwa
Tankokin jigilar mai na tafiya a gaɓar teku, kusa da mashigin ruwan Hormuz, ranar 11 ga watan Maris, 2026 [TSOHON HOTO]. / Reuters / Reuters
7 awanni baya

Ƙarar fashewar abubuwa ta karaɗe Beirut da sanyin safiyar ranar Litinin yayin da Isra’ila ta kai hari kan babban birnin na Lebanon.

Ta kuma kai jerin sabbin hare-hare kan Tehran, yayin da Dubai ta rufe filin jiragen samanta na wucen gadi ala tilas bayan wani jirgi mara matuƙin Iran ya afka wa wata tankar mai.

Tun lokacin da Amurka da Isra’ila suka fara kai mata hari kimanin makonni biyu da suka gabata, Iran ta fara kai hare-hare babu ƙaƙƙautawa kan Isra’ila da sansanonin Amurka da da kuma kayayyakin makamashi na maƙwabtanta ƙasashen Larabawa da ke gaɓar teku ta hanyar mafani da jirage mara matuƙa da makamai masu linzami.

Ta kuma katse jigilar kayayyaki ta mashigin ruwan Hormuz, ta inda ake jigilar kashi ɗaya cikin biyar na man duniya, lamarin da ya haddasa fargaba da ke ƙaruwa na rikicin makamashi na duniya da kuma matsa wa Washington yayin da masu amfani da makamashin suka fara jin zafinsa a gidajen mai.

Brent crude, wadda ita ce kasuwar ma’aunin farashin mai ta duniya, ta haƙiƙance kan kuɗi fiye da $100 kan kowace gangar ɗanyen mai ranar Litinin.

Da farkon fara cinikayya dai farashin na kan $104 ne, inda ya haura da kashi 45 cikin 100 tun da Amurka da Isra’ila suka kai hari kan Iran ranar 28 ga watan Fabrairu. Ya tashi zuwa kimanin $120 a cikin rikicin.

Shugaba Donald Trump ya ce shi ya buƙaci ƙasashe bakwai su tura jiragen yaƙinsu na ruwa domin tabbatar da cewa Mashigar Ruwan Hormuz na a buɗe, amma kiraye-kirayensa ba su janyo alƙawurra ba.

Jam’iyyarsa na ƙara nuna damuwa cewa tashin farashin kayayyaki ga Amurkawa masu amfani da abubuwa zai ji wa ‘yan Republican ciwo a zaɓen kakar da ke tafe.

“Ina neman waɗannan ƙasashen su shigo su kare ƙasashensu, saboda ƙasashensu ne,” kamar yadda Trump ya shaida wa manema labarai yayin da yake komawa Washington daga Florida kan jirgin shugaban ƙasar Amurka, Air Force One.

Bai bayyana sunayen ƙasashen ba, amma a baya ya yi kira ga China da Faransa da Japan Koriya ta Kudu da kuma Birtaniya .

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana iƙirarin cewa za ta iya yiwuwa cewa ƙasarsa na neman yadda za tattauna kawo ƙarshen yaƙin a matsayin “yaudara,” yana mai bayyana a wani saƙon da ya wallafa kafafen sada zumunta da safiyar ranar Ltinin cewa ƙasarsa ba ta neman “sulhu ko tattaunawa.”

“Dakarun sojinmu masu ƙarfi za su ci gaba da wuta har sai lokacin da shugaban Amurka ya gane cewa yaƙin da ya saɓa wa doka da yake ƙaƙaba wa ‘yan Iran da Amurkawa bai dace ba kuma dole kada a sake maimata shi,” kamar yadda ya rubuta a shafin X.

Iran ta kai hari kan filin jiragen saman Dubai

Yayin da safiya ke yi ranar Litinin, wani jirgi mara matuƙi ya afka wa wata tankar mai kusa da filin jiragen sama na ƙasa da ƙasa na Dubai, filin jiragen sama da ya fi yawan jigilar matafiya daga wata ƙasa zuwa wata ƙasa, lamarin da ya haddasa wata babbar gobara.

‘Yan kwana-kwana sun samu sun shawo kan wutar, kuma ba a samu wani rahoton jin rauni ba, amma filin jiragen saman ya dakatar da tashi da sauƙan jirage na wucen gadi.

Iran ta harba ɗaruruwan makamai masu linzami da jirage mara matuƙa zuwa ƙasashen Larabawa da ke gaɓar teku da ke karɓar baƙuncin kayayyakin sojin Amurka tun lokacin da aka fara yaƙin.

Hukumomin Haɗaɗɗiyar Daular Larabara sun ce tsarin tsaron sararin samaniyarsu ya kakkaɓo yawancinsu, duk da cewa ɓaraguzansu da kuma wasu jirage mara matuƙa sun faɗa cikin ƙasar.

kwanan nan jami’an Iran sun zargi Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da bari a yi amfani da ƙasarta domin kai hari kan Iran.

Jami’an Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun yi watsi da zarge-zargen a matsayin ƙarya inda suka ce matakan ƙasar sun kasance na kare kai ne.

Ita kuwa ƙasar Saudiyya ta ce ta kakkaɓo jerin ƙarin jirage mara matuƙa da aka tura zuwa yankin gabshinta , inda manyan kayayyakin mai suke.

Sojin Isra’ila ta ce da farkon ranar Litinin Iran ta harba makamai masu linzami zuwa ta Isra’ila ma.

Isra’ila ta ce Iran tana harba bam mai tarin bama-bamai waɗanda za su iya kauce wa tsarin tsaron sararin samaniyarta da kuma watsa ƙananan makamai zuwa wurare daban daban.

Isra’ila ta kai hari Beirut da Tehran

An ji ƙara mai yawa a Beirut yayin da Isra’ila ta ƙadamar da sabbin hare-hare kan babban birnin na Lebanon kafin safiya, inda ta yi iƙirarin cewa tana kai hari ne kan kayayyaki masu alaƙa da Hezbollah.

Sojin Isra’ila ta ba da umarnin ƙauracewa ga unguwanni da dama a Beirut da kuma kudancin Lebadon. Zuwa yanzu, fiye da mutum 800,000 ne hare-haren Isra’ila a Lebanon suka raba da gidajensu .

Aƙalla mutum 850 ne hare-haren Isra’ila suka kashe kawo yanzu, ciki har da ƙananan yara 107 da mata 66.

Jim kaɗan bayan sojin Isra’ila ta yi shelar ƙaddamar da sabbin hare-hare kan ababe a Tehran , an ji fashewar abubuwa a babban birnin na Iran da kuma wurare da ke kusa.

Fiye da mutum 1,300 ne aka kashe kawo yanzu a Iran, in ji ƙungiyar ba da agaji ta Red Cross.

A Isra’ila, mutane 12 ne makamai masu linzamin iran suka kashe ,kuma ƙari sun jikkata , ciki har da uku da suka ji rauni ranar Lahadi.

Aƙalla sojin Amurka 13 ne suka mutu , shida daga cikinsu sun mutu ne a hatsarin jirgi a Iraƙi a makon da ya gabata .

Trump ya yi barazanar ‘tunawa’ game da ƙawayen da ba su taimaka ba

A kan jirgi On Air Force One, Trump bai bayyana wace ƙasa ce za ta kasance cikin gamayyar da yake son ta sa ido kan mashigin ruwan Hormuz ba domin samar da tsaro ga tankokin mai da sauran jiragen dakon kayayyaki da ke wucewa .

Amman ya ce ba zai manta ƙasasehn da suka ƙi taimakawa ba. Ya ambaci Firayim Ministan Birtaniya Keir Starmer, wanda da farko ya ƙi ya saka jiragen ɗaukar jiragen yaƙin Birtaniya “cikin hatsari.”

“Ko mun samu taimako ko bamu samu ba , zan iya faɗan wannan, kuma ina gaya musu: za mu tuna,” in ji Trump.

Ranar Litinin, Firayim Ministan Japan Sanae Takaichi ta shaida wa majalisar dokokin ƙasar cewa gwamnatinta “ba ta ji komai ba” daga Washington game da kiran Trump kan jiragen ruwa na taimakawa domin kare mashigin ruwan Hormuz.

Sai dai kuma Japan na shigar da fiye da kashi 90 cikin 100 na ɗanyen manta daga Gabas Ta Tsakiya ne, kuma ta ce an yi tattaunawa game da abin da za a iya yi domin kare jiragen ruwan japan “ba tare da la’akari da buƙatar Amurka ba.”

Ministan Tsaro Shinjiro Koizumi ya ce ba shi da wani shiri na tura jiragen yaƙi na ruwa zuwa mashigin Hormuz a ƙarƙashin yanayin kariya na yanzu.

Ranar Litinin ne Japan ta fara fitar da mai daga runbun ajiyarta domin magance damuwa game da ƙarancin mai da tashin farashi.

Trump ya yi hasashen cewa farashin mai zai sauƙa, amma bai ba da amsa kai-tsaye ba kan ko gwamnatinsa tana tattaunawa game da sayar da takardar yarjejeniyar sayar da mai nan gaba domin hana tashin farashin mai, wani abin da sakataren harkokin cikin gidansa ya bayyana a matsayin abu mai yiwuwa.

“Farashin za su faɗo yayin da ya ƙare. Kuma zai ƙare da wuri,” kamar yadda ya shaida wa manema labarai.