Hukumar ƙwallon ƙafar Afirka (CAF) ta ce kocin Nijeriya, Eric Chelle shi ne gwarzon koci a zagayen rukuni na gasar AFCON 2025, yayin da shi ma ɗanwasan Nijeriya, Ademola Lookman ya zama gwarzon ɗanwasan tsakiya da ya fi nuna bajinta.
CAF ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar kan jerin zaratan ‘yanwasa 11 da kocin da ya fi nuna bajinta wajen jagorantar tawagarsa bayan buga jimillar wasanni 36 a zagayen rukuni.
Daga ‘yanwasan akwai golan Masar, Mohamed El Shenawy, da Riyad Mahrez na Aljeriya, da Sadio Mané na Senegal, da Amad Diallo na Ivory Coast.

Daga tawagar Super Eagles ta Nijeriya, Ademola Lookman aka zaɓa a matsayin ɗanwasan tsakiya mai kai hari daga gefen hagu. Lookman ya ci ƙwallo 2 a wasanni 3 da ya buga zuwa yanzu.
Gwarzon koci
Tawagar Nijeriya ta ƙare zagayen rukuni da maki 9, saboda ta ci duka wasanninta 3, inda ta kara da Tanzania ta ci 2-1, sai Tunisia da ta ci 3-2, sannan Uganda, wadda ta doke da ci 3-1.
Wannan nasara ta Nijeriya, wadda Aljeriya ce kawai cikin sauran ƙasashe 23 ta samu maki 9 a rukuni, ya sa an karrama kocin Super Eagles, Eric Chelle a matsayin gwarzon koci a zagayen.
Chelle ya yi ƙoƙari wajen jagorantar Nijeriya wajen cin jimillar ƙwallaye 8, wanda shi ne mafi yawa da wata tawaga ta ci a gaba ɗaya zagayen.
Kocin na jan ragamar Super Eagles a wata babbar gasa a karon farko, tun bayan da aka ba shi muƙamin jagorantar tawagar a Janairun 2025.
A makon nan ne aka kammala zagayen rukuni na gasar kofin ƙasashen Afirka na AFCON 2025 wanda ake yi a Maroko, inda tawagogi daban-daban suka ƙayatar.






