Ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta yi watsi da jadawalin da sojojin Guinea-Bissau suka tsara na miƙa mulki ga gwamnatin farar-hula, inda ta yi kira da su yi gaggawar miƙa mulki, kana ta yi gargaɗin sanya takunkumai kan masu yi wa tsarin mulki ƙafar-ungulu a ƙasar.
Sojojin Guinea-Bissau sun hamɓarar da gwamnatin Umaro Sissoco Embalo ranar 26 ga watan Nuwamba inda suka ɗora Manjo-Janar Horta Inta-A a matsayin shugaban gwamnatin rikon ƙwarya kwana ɗaya bayan haka.
Juyin mulkin Guinea-Bissau shi ne na tara da aka yi a ƙasashen Yammaci da Tsakiyar Afirka a cikin shekara biyar, lamarin da ya ƙara jefa fargaba a zukatan jama’a game da makomar mulkin dimokuraɗiyya a yankin wanda ke fama da rashin tsaro da rikice-rikicen siyasa.
Shugabannin ƙasashen ƙungiyar ECOWAS sun gudanar da taronsu na shekara-shekara a Abuja, babban birnin Nijeriya inda suka yi kira da a gaggauta sakin ‘yansiyasa da aka tsare, cikinsu har da jagororin jam’iyyun hamayya, kana suka dage cewa dole a miƙa mulki ga gwamnatin farar-hula cikin ƙanƙanin lokaci a Guinea-Bissau.
"Matsayar da shugabannin ECOWAS suka cim ma ita ce ba za a lamunci juyin mulki ba," a cewar Omar Touray, shugaban hukumar ECOWAS.
ECOWAS ta ce masu sanya ido daga ƙungiyar da ƙungiyar Tarayyar Afirka da kuma ƙungiyar ƙasashen da Portugal ta yi wa mulkin mallaka sun tabbatar da sahihancin zaɓen da aka gudanar a Guinea-Bissau ranar 23 ga watan Nuwamba.
Kazalika ECOWAS ta umarci shugabanta ya jagoranci wata babbar tawaga zuwa Guinea-Bissau domin tattaunawa da sojojin da suka yi juyin mulki.
Muddin sojojin suka ƙi amincewa da buƙatar ECOWAS, za a ƙaƙaba takunkumai kan wasu shugabannin soji da ƙungiyoyi da ke yin ƙafar-ungulu a ƙoƙarin mayar da mulki hannun gwamnatin farar-hula, in ji ƙungiyar, inda ta yi kira ga ƙungiyar Tarayyar Afirka da sauran masu ruwa da tsaki da su goyi bayan matakin da take shirin ɗauka.












