Gwamnatin ƙasar Ghana ta kama ‘yan Nijeriya 32 da ke zama a ƙasar kan zargin damfara ta intanet.
Ministan sadarwa da fasahar intanet na ƙasar, Sam George, ya bayyana a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X cewa an kama ‘yan Nijeriyan ne yayin da suke kitsa damfarar intanet ta salon yin soyayya.
Jami’an hukumar tsaron intanet ta Ghana (CSA) sun kai samame kan mutanen da ake zargin ne da sanyin safiyar ranar Asabar a garin Kosoa Tuba a lardin arewacin ƙasar.
“A wannan safiya, an sake cin galaba a kan laifukan intanet a ƙasar Ghana. Wani aikin haɗin gwiwa tsakanin hukumarmu da hukumar tsaro ta ƙasa ya sa an kama ‘yan Nijeriya 32 da suke kitsa damfarar soyayya a Kasoa Tuba,” kamar yadda Mista Sam ya rubuta.
Ya ce an kai samamen ne bayan samun bayanan sirri domin tabbatar da cewa Ghana ba ta kasance dandalin masu aikata laifukan intanet ba.
“Za mu ci gaba da tallafa wa hukumar a ƙoƙarinta na matsa ƙaimi yayin da muke fafutukar ganin Ghana ba ta zama wurin da laifukan intanet ba ke samun gindin zama ba,” in ji shi.
Wannan shi ne kame na baya bayan nan da jami’an tsaron Ghana suka yi wa ‘yan Nijeriya a wani yunƙuri na yaƙar laifukan intanet.
A watan da ya gabata, jami’an hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin azrikin ƙasa ta’annati ta Ghana (EOCO) sun kama ‘yan Nijeriya 7 a Accra, babban birnin ƙasar, bisa laifin damfara ta intanet.
Watanni uku da suka gabata, jami’an sun kama kimanin ‘yan Nijeriya 50 bayan sun samu bayanan sirri da suka nuna safarar mutane da laifukan intanet.













