Mummunan tashin hankali ya ɓarke a ranar Asabar tsakanin ‘yantawayen M23 da sojojin da ke goyon bayan gwamnati a wasu garuruwa da ke kewaye da birnin Uvira mai muhimmanci a gabashin Jamhuriyar Dimokiradiyyar Kongo, in ji majiyoyi na cikin gida.
Gabashin na Jamhuriyar Dimokiradiyyar Kongo mai arziki, wanda ke iyaka da Rwanda da Burundi, ya shafe shekaru 30 yana fama da tashin hankali marar yankewa.
Al'amuran sun kara tsananta tun daga 2021 saboda dawowar kungiyar M23.
Bayan ta kwace manyan biranen gabas biyu, Goma da Bukavu, a karshen bara, kungiyar ta kaddamar da sabon farmaki a watan Disamba a lardin Kivu ta Kudu kuma ta karbe iko ranar 10 ga Disamba da Uvira, birni mai muhimmanci da ke da daruruwan dubban mutane, kusa da Burundi, mai kawance da DRC.
Sulhu da Trump ya shiga tsakani
Kungiyar ta kuma ƙwace iko da wasu yankunan kan iyaka a daidai lokacin da DRC da Rwanda ke sanya hannu kan wata yarjejeniyar sulhu a Washington wacce Shugaba Donald Trump na Amurka ya shiga tsakani wajen ƙulla ta.
Tun daga karfe 3 na dare (0100 GMT), an bayar da rahoton rikici mai zafi tsakanin 'yan tawaye na M23 da Wazalendo (dakarun da ke goyon bayan Kinshasa) da kuma rundunar sojin Jamhuriyar a wasu wurare a yankin Uvira, a lardin Kivu ta Kudu, in ji Kelvin Bwija, mai tsara al'umma na Uvira, kamar yadda ya shaida wa AFP.
Bwija ya ambaci garuruwan Kashombe, Lubanda, Musingwe, Katongo, da Kigongo, waɗanda suke kusan kilomita 10 daga birnin, a matsayin wuraren da ake fafatawa.
'Yanzu haka ana jin karar harbe-harbe a Uvira,' in ji shi.
Wani mazaunin Kigongo, wanda aka same shi ta waya, ya tabbatar wa AFP cewa 'rikicin ya sake barkewa a safiyar yau, ana jin manyan fashe-fashe da harbe-harbe'.
Laftanar Reagan Mbuyi Kalonji, kakakin rundunar sojin Kongo (FARDC) na yankin, ya tabbatar wa AFP da cewa ana 'gabza fada a Kigongo da Katongo, musamman a tsaunukan Kashombe da Lubanda a yankin Uvira'.
Mata da yara sun jikkata
M23 ta sanar a ranar 17 ga Disamba cewa za ta janye daga Uvira, tare da roƙon masu shiga tsakani su tabbatar da kariyar birnin daga tashin hankali da kuma 'sake mayar da sojoji'.
An kuma bayar da rahotanni na rikici mai tsanani a lardin Kivu ta Arewa mai makwabtaka tun ranar Jumma'a, inda aƙalla mutane shida suka rasa rayukansu kuma 41 suka ji rauni a wani harin bam da aka danganta wa rundunar sojin Kongo a karamar hukumar Masisi a lardin Kivu ta Arewa, a cewar majiyoyi na cikin gida.
Médecins Sans Frontières (MSF) ta bayyana a shafukan sada zumunta cewa 'mutane 42, ciki har da yara da mata da dama sun ji rauni daga abubuwa masu kaifi da wasu raunuka, an kawo su Babban Asibitin na Masisi bayan harin jirgin sama a yankin da jama’a ke zama a Masisi'.
MSF ta ƙara da cewa biyu daga cikin waɗannan mutane sun mutu.













