A babban taron Majalisar Dinkin Duniya a wannan makon, duniya ta taru saboda daya daga cikin lokuta mafiya mahimmanci a siyasar kasa kasa.
Shugabanni daga kasashe kusan 200 sun yi magana game da yaki, yunwa da kuma makomar duniyarmu. Bigire ne da yake neman diflomasiyyar gaggawa da irin shugabancin da duniya ke bukata.
Shugaba Donald Trump ya yi jawabi a ranar Talata na kusan awa daya. A cikin waɗancan lokutan da duniya ta mayar da hankali a kai, ya yanke shawarar yin amfani da matsayinsa don sukar magajin garin Landan, Sadiq Khan.
Ya bayyana cewa Turai tana "fada wa halaka" kuma ya zargi Khan da kawo "dokar Shari'a" zuwa Landan.
Wannan ba tuntuben harshe ba ne. Zabi ne. Jagora mafi iko a duniya ya zaɓi ya tabo batun ɗaya daga cikin tsofaffin almarori na kyamar Musulunci: cewa shugabancin Musulmi yana nuni da shigar da tsarin shari'ar Musulunci.
Biritaniya tana da tsarin shari'a da ba ruwan sa da wani addini. Majalisun Shari'a suna wanzuwa ne kawai a cikin ƙayyadadden wurare don bayar da shawara ba wai don kawao wata doka da za a yi aiki da ita ba.
Don kawo labarin da ba na gaskiya ba, saboda a dawwamar da labarin karya da aka dade ana amfani da shi wajen bayyana Musulmi a matsayin barazana ga rayuwar al’umma da kuma nuna shakku kan halaccinsu a mukaman gwamnati.
A jawabinsa na wannan makon, ya kira shi da "mummunan magajin gari," amma ba shi ne karon farko da Trump ya muzanta Khan a kalaminsa ba.
A 2019, ya yi masa lakabi da "asararre" kuma ya zarge shi da gazawa a Landan. Abin da ya janyo waɗannan sukar ba aiki a ofis ba ne, sai don wane ne shi.
Gyara a bayyane yake. Trump ya sa Khan a gaba ne saboda shi Musulmi ne.
Shi kansa Khan ya fito fili a ya yi bayani a kan wannan. Da aka tambaye shi game da munanan kalaman Trump na baya-bayan nan, ya amsa da cewa: "Ina jin Shugaba Trump ya nuna cewa shi mai nuna wariyar launin fata ne, shi mai nuna wariya ne, mutum ne da ya tsani mata, kuma mai kyamar Musulunci ne."
A wajen magajin garin ɗaya daga cikin manyan biranen duniya, wannan ba zuki tamalli ba ne. Yana bayyana abu yadda yake karara.
Sadik Khan ne ke jagorantar Landan tsawon shekaru takwas. A lokacin, ya kasance ɗaya daga cikin biranen da aka fi ziyarta a duniya, yana jan hankalin baƙi da masu saka hannun jari na Amurka fiye da kowane babban birni a Turai.
Don nuna cewa batun ya faɗo ƙarƙashin "Tsarin Shari'a" ba shi da tushe. Amma manufar a bayyane take: nuna cewa shugaban lardi Musulmi ba halastaccen shugaba ba ne.
Waye mutum na sama da adalci
Wannan sakon bai tsaya a matakin furucin kawai ba. Mun ga inda ya isa. A lokacin bazarar 2024, tarzoma ta barke a Birtaniya.
Bata-gari sun yi tattaki a garuruwa suna rera taken nuna kyama ga Musulmi, suna kai hari kan Masallatai, suna lalata wuraren kasuwanci na Musulmi, da kuma kai hari a otal-otal da ke dauke da masu neman mafaka.
Iyalai sun bayyana rayuwa cikin dare da tsoro da tashin hankali. Tashin hankalin ya samo asali ne saboda yada labaran karya, amma ya bayyana wani abu mai zurfi: yadda karya game da Musulmai ke saurin iya haifar da rikici.
Bayan shekara guda, wannan labarin ya sake koma wa kan wani babban mataki. A watan Satumban 2025, sama da mutane 100,000 ne suka yi maci ta tsakiyar Landan don nuna goyon bayansu ga Tommy Robinson.
Wannan ne ɗaya daga cikin manyan tarurrukan masu tsaurin ra’ayi da aka shaida kwanan nan.
Jawaban sun zama masu tayar da hankali. Dan siyasar Faransa Eric Zemmour ya shaida wa taron cewa suna fuskantar "babban maye gurbi" na bakin haure Musulmi.
Dan majalisar dokokin Belgium Philip Dewinter ya bayyana cewa: "Musulunci makiyinmu ne na hakika, dole ne mu kawar da Musulunci."
Wata mai sharhi ‘yar kasar Holland Eva Vlaardingerbroek, ta yi magana kan “fyade, maye gurbin matsugunan jama’a, da kuma kisan kai.
Elon Musk ya bayyana ta hanyar sakon bidiyo. Allunanan aike wa da sakonni a wajen taron sun yi wa Sadiq Khan lakabi da "wakilin barci."
Shugabannin addinai sun yi kira da a haramta Masallatai, abinci na halal, da hijabai, suna bayyana wannan a matsayin "yakin addini." An cisge tutocin Falasdinawa a dandalin da aka yi taron.
'Yan sanda sun ba da rahoton "tashin hankali da ba za a yarda da shi ba" bayan an kai wa jami'an hari da kwalabe, da harsunan wuta, da kuma kutufo.
A wajen Musulman Birtaniya, wannan ba siyasa ba ce irin ta wasan kwaikwayo. Lamari ne na gaske da ke afku wa yau da kullum.
A makonnin baya-bayan nan an lalata Masallatai. An ga jikin bangwaye dauke da rubutun "Dakatar da Musulunci, dakatar da jiragen ruwa."
Al'umma na tsaurara matakan tsaro. Iyalai sun fi bayar da muhimmanci ga zaman su da amincinsu. Illar ita ce bayyana Musulmai a matsayin al'ummar da ake zargi, wadanda ake wa zama da su kallon mai dauke da wasu sharudda.
Sanannu irin su Nigel Farage sun ƙara ruruta wutar wannan yanayin da aka shiga. Ya mamaye kafofin watsa labarai, yana gabatar da kansa a matsayin babbar murya, duk da haka maganganunsa a kai a kai suna bayyana gudun hijira wa samun al’ummu daban-daban a waje guda a matsayin matsaloli.
Ta hanyar ayyana wanda yake namu da wanda ba namu ba, ya haifar da yanayin da ya kawo bullar karin masu tsaurin ra’ayi da dama.
Wannan shi ne yadda ake karkatar da hankalan jama’a game da maganganun da suka mamaye kafafen yada labarai.
Kuma wannan bai takaita ga Birtaniya kadai ba. A duk faɗin Turai, jam'iyyun masu tsaurin ra’ayi suna karuwa. Marine Le Pen ta Faransa, Jam’iyyar Alternative für Deutschland a Jamus, da sauran su ba sa yin motsi.
A wasu lokuta, gwamnatoci da kansu sun yi amfani da manufofin nuna wariya waɗanda ke halasta manufofi iri ɗaya da na masu tsaurin ra’ayi.
Tsatsar nuna kyamar Musulunci a duniya
Alakar mayar da batun ga Trump a fili take. Lokacin da shugaban Amurka ya tsaya a mataki mafi girma a duniya kuma ya maimaita makircin kyamatar Musulunci, hakan na aike wa da sakonni.
Sakon na kuma gaya wa ƙungiyoyin masu tsaurin ra’ayi cewa ba su da iyaka. Yana gaya wa ’yan siyasar da suke rangwada da rarrabuwar kawuna cewa za su samu skaamako mai kyau, ba wai fuskantar hukunci ba.
Haka kuma yana koya wa gwamnatoci cewa za a iya murda ƙiyayya a shigar da ita siyasar yau da kullum.
Trump ya kuma yi amfani da jawabinsa na Majalisar Dinkin Duniya wajen yin magana game da Gaza.
Ya gargadi kasashe game da amince wa da Falasdinu, yana mai cewa hakan zai "karrama Hamas." Amma duk da haka amince wa da Falasdinu na karuwa, kuma ana ci gaba da tashe-tashen hankula.
Tattaunawar ta yi tsauri: a daidai lokacin da ake fama da bala'in rikicin jin kai, shugaban ya zaɓi ya mai da hankali kan tozarta magajin gari Musulmi a Landan. Nuna kyama ga Musulunci a nan ba arashi ba ne.
Kalubalen da ke gaban Birtaniya da Turai shi ne ko za a bar wannan yanayi ya kara tsauri. Tashe-tashen hankula, tarzomar jama'a, rubuce-rubucen batanci da barna a cikin Masallatai ba sabbin abubuwa ba ne.
Daduwar nuna kyama ga Musulunci ba ya karfafa Turai. Yana rauna ta nahiyar ne, yana haifar da rarrabuwar kawuna a lokacin da ake bukatar jagoranci cikin gaggawa.
Dole ne Firaministanmu ya kasance tsayayye. Nuna kyama ga Musulunci ba batu da za a ware gefe guda ba. Haɗari ne ga lafiyar jama'a da rayuwar dimokuraɗiyya.
Dole ne a fuskanci batun cikin gaggawa kamar kowane nau'i na ƙiyayya. Kuma sama da magana da baki, dole ne gwamnati ta fitar da ingantaccen labari na kasa wanda dukkanin sassan al'umma ke alfahari da shi.
Duniya na buƙatar jagorancin da zai fuskanci rikice-rikice da gaske: kawo ƙarshen wahala a Gaza, magance gudun hijira, talauci, da illolin sauyin yanayi.
Ba za a iya ƙyale kyamar Musulunci ya zama harshen karkatar da hankali, ko karkacewa, ko fake wa da guzuma a harbi karsana ba.