| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Uganda za ta sallami majinyacin Ebola na ƙarshe
Za a iya ayyana ƙasar a matsayin wadda ba ta da Ebola idan ba a samu sabbin rahotanni na mutanen suka kamu da cutar ba a cikin kwanaki 42 na sa idon Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).
Uganda za ta sallami majinyacin Ebola na ƙarshe
Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi kira da a tallafawa yankuna don yakar cutar Ebola
 

Uganda na shirin sallamar majinyacin Ebola na ƙarshe a ranar Alhamis, wanda hakan ke nuna rana ta farko ta soma ƙidayar kwanaki 42 kafin a ayyana ƙasar a matsayin wacce ba ta da cutar Ebola, kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin ƙasar ya bayyana.

A ƙarƙashin tsarin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), za a iya ayyana ƙasa a matsayin wadda ta fita daga cikin jerin masu ɗauke cutar Ebola idan ba a samu sabbin alƙaluma na mutanen da suka kamu da cutar ba a tsawon kwanaki 42 a jere, bayan sallamar mutum na ƙarshe wanda aka tabbatar ya warke daga cutar.

 Uganda ta kai matakin ƙarshe na ɓarkewar cutar

Ma'aikatar Lafiya ta Uganda ta ce marasa lafiya daga cutar Ebola 17 sun warke, inda mutum ɗaya da aka keɓe ya rage kana an samu rahoton mutuwar mutane biyu.

Sannan an samu mutane biyar da suka kamu da cuta a cikin gida, yayin da 15 kuma suka shiga ƙasar da cutar.

Mai magana da yawun gwamnatin ƙasar Alan Kasujja ya ce za a sallami majinyaci na ƙarshe daga Asibitin Kula da Lafiya na Mulago da ke babban birnin Kampala, ranar Alhamis.

"Idan hakan ta faru, Uganda za ta soma ƙirga kwanaki, " kamar yadda Kasujja ya wallafa a shafinsa na X.

Ya ƙara da cewa "Idan kwanaki 42 suka wuce ba tare da an samu wani sabon mutum da ya kamu da cutar ba, Hukumar WHO za ta ayyana mu a matsayin ƙasar da ba ta da cutar Ebola."

Ƙasar da aka fi samu barkewar cutar, wadda WHO ta ayyana ta kai matakin gaggawa ta lafiyar jama'a wato Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) a watan Mayu, ta samu mutane 2,011 da aka tabbatar sun kamu da cutar da mutuwar mutane 754 ya zuwa ranar Labaran nan, a cewar alƙaluman gwamnatin ƙasar ta Congo.

Duk waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar suna da alaƙa da nau'in ƙwayar cutar Bundibugyo da ba a saba gani ba, wanda WHO ta bayyana a matsayin annobar cuta ta uku mafi girma a tarihi.

Rumbun Labarai
Ghana ta ba da shawarar fara amfani da kuɗin ECO a matakai tsakanin ƙasashen ECOWAS da suka shirya
Sojojin Sudan sun sami ƙarin wurare a jihar West Kordofan yayin da mayaƙan RSF ke ja da baya
Shugaba Tiani na Nijar ya nada Aboubacar Issaka a matsayin sabon shugaban ’yansandan kasar
Ghana na samun tan 62 na sinadarin mercury a kowace shekara ta hanyoyin da ba su dace ba
Rundunar tsaron Nijar ta ƙwace makamai da ake zargin ana shirin kai wa Boko Haram a Diffa
Gwamnatin Nijar ta haramta fitar da gyaɗa zuwa ƙasashen waje
Sudan ta Kudu ta sake dage babban zaben kasar zuwa ranar 11 ga Fabrairun 2027
Amurka za ta sa ido sosai kan zaben shugaban kasar Nijeriya na watan Janairu - Jami’i
An kashe fararen-hula akalla 37 a wani harin kwanton-ɓauna a yammacin Jamhuriyar Nijar
An kashe aƙalla mutum 10 yayin da dakarun tsaron Guinea suka yi arangama da masu haƙar zinare
Ghana za ta kashe dala miliyan 200 kan shirya wa gina tashar makamashin nukiliya
Ghana ta kaddamar da sabuwar takardar kudi ta Cedi
Burhan na Sudan ya buƙaci a cire siyasa a rabon tallafin yaƙi da sauyin yanayi ga ƙasashe mara ƙarfi
Greenpeace ta gargaɗi Ghana kan barazanar shara sakamakon shigo da tsofaffin tufafi miliyan 1 a mako
Yadda El Niño ke sake haifar da ɓarkewar cutar Zazzaɓin Rift Valley a Gabashin Afirka
BAMEX 2026: An fara baje-kolin fasahar tsaro ta ƙasa da ƙasa a Mali
Kotu a DR Congo ta yanke wa sojoji 66 hukuncin kisa saboda 'ja da baya a fagen daga'
Kwale-kwale dauke da ‘yan ci-rani ya kife a kusa da Senegal, mutum 21 sun rasu, in ji hukumomi
An yanke wa jagoran ƙungiyar asiri a Kenya hukuncin ɗaurin shekara 200 kan kisan yara 190
MƊD ta yi gargaɗin cewa El Nino za ta iya raba mutum miliyan uku da gidajensu a Gabashin Afirka