| Hausa
Ra'ayi
AFIRKA
6 minti karatu
Djibouti: Ƙaramar ƙasar Afirka mai girman ikon diflomasiyya
A yankin kusurwar Afrika, inda illar ƙarancin tsaro da rikici ta munana, ikon Djibouti na sasantawa ya samar da damarmakin tattaunawa, da tabbatar da dangantakar ƙasashen duniya cikin daidaito.
Djibouti: Ƙaramar ƙasar Afirka mai girman ikon diflomasiyya
Gabashin teku na Jibuti, a fadin Mashigin Bab-el-Mandeb, wani kunkurun mashigin ruwa ne da ke hada Jan Teku da Tekun Aden. / Reuters
8 Disamba 2025

Yankin da Djibouti take yanki ne mai fama da rikici, sauyin ƙawance, da rashin tabbas na siyasa. Sai dai ƙasar ta zamo ƙasa guda mafi zaman lafiya, a yankin Kusurwar Afirka sakamakon yadda ta nuna tabbaci a fannin diflomasiyya mai ɗorewa.

A matakin Tarayyar Afirka, Djibouti tana ci gaba da tallafawa sasanci da shirye‑shiryen zaman lafiya. Ta hanyar goyon bayan tsare‑tsaren da AU ke jagoranta ko samar da yanayi mai dacewa don yin musayar miyau, ƙasar ta daidaita kanta a matsayin bigire a lokutan rikici a Sudan, Somalia, Habasha, da kuma a bakin Bahar Maliya.

Wannan daidaito na da muhimmanci musamman yayin da Sudan ke fuskantar ɗaya daga cikin manyan rikicin jinƙai a duniya. Djibouti ta kasance mamba na Kwamitin Zaman Lafiya da Tsaro na Tarayyar Afirka sau da yawa, inda ta kasance a ofis har zuwa Maris 2025.

Diflomasiyyar yanki da sasanci

Djibouti tana zama masaukin hedikwatar IGAD (Hukumar Haɗin Gwiwar Gwamnatoci Don Cigaban), wata ƙungiyar yanki a Gabashin Afirka wadda ta ƙunshi ƙasashe mambobin da suka haɗa da Djibouti, Eritrea, Habasha, Kenya, Somalia, Sudan ta Kudu, Sudan, da Uganda.

Sau da yawa ƙasar ta taka rawar mai sasanci ta yanki. Misali, ta karɓa kuma ta ɗauki nauyin Taron Sulhu na Arta Somalia a shekarar 2000, wanda ya taimaka aka kafa gwamnati ta yanzu ta Somalia bayan rushewar mulkin soja a 1991, da kuma yaƙin basasa da ya biyo baya.

A 2008, Djibouti ta sasanta tsakanin gwamnatocin wucin-gadi na tarayya na Somalia da Ƙawance ‘yan adawa ta Alliance for the Re‑liberation of Somalia, abin da ya kai ga kafuwar gwamnatin haɗin-kan kasa a shekarar da ta biyo baya.

Bugu da ƙari, sau biyu Djibouti ta sasanta tattaunawa tsakanin Gwamnatin Tarayya ta Somalia da shugabannin Somaliland—wanda ya ayyana kansa a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta— a 2020, sannan a 2023.

Waɗannan ƙoƙari sun nufi dawo da tattaunawa ta hukuma kan batutuwan da suke da moriya ga kowa, inda Amurka da Tarayyar Turai suka kasance masu tallafawa.

Djibouti tana bayar da sojoji ga AIMIS/ATMIS (Rundunar Mika Mulki ta Tarayyar Afirka a Somalia), kuma tana taka rawar gani a yaƙi da ƙungiyar ta’addanci ta Al‑Shabaab, wadda ke barazana ga Somalia da maƙwabtanta.

Djibouti ta kuma nemi sasanta rikicin Sudan. A 2023, Shugaban ƙasar ya karɓi jagorancin karɓa-karɓa na IGAD, wanda ya kai ga tattaunawa a watan Disamba a Djibouti tsakanin Janar Abdel Fattah al‑Burhan, Shugaban Majalisar Mulkin Wucin-gadi ta Sudan, da Janar Mohamed Hamdan Dagalo (“Hemedti”) na Rundunar Tallafin Gaggawa ta RSF.

Ko da yake rikicin ya ci gaba, Djibouti ta ci gaba da neman warware shi cikin lumana tare da buɗe hanyar tallafin jinƙai ba tare da hani ba.

A 2023–2024, harin ‘yan Houthi daga Yemen ya tilasta wa jiragen ruwa da yawa kauce wa tashar Bab el‑Mandeb da Bahar Maliya, abin da ya zama barazanar kai-tsaye ga tattalin arziƙin Djibouti.

Ta amfani da matsayinta na jagorancin IGAD da kuma wurin da take na kusan kilomita 20 daga Tekun Larabawa, Djibouti ta yi ƙoƙarin yin tasiri a abubuwan da ke faruwa a Yemen, abin da ya samo asali daga zuwan ‘yan gudun hijira na Yemen da kuma manyan dalilan tattalin arziƙi.

Haɗin-gwiwar diflomasiyya don warware matsaloli yanki

Muhimmancin diflomasiyyar Djibouti ya ƙaru a fili lokacin da ta karɓi taron Bita na Ministoci Karo na Uku tsakanin Turkiyya da Afirka a 2024.

Wannan taro ya ƙara nuna matsayin Djibouti na wuri mai aminci don tattauna dabaru tsakanin Afirka da Turkiyya kan kasuwanci, tsaro, taimakon jinƙai, da daidaituwar siyasa.

Muhawarori a babban mataki sun haɓaka Shirin Ayyukan Hadin-Gwiwa tsakanin Afirka da Turkiyya na 2022–2026, suna daidaita shi da Agenda 2063 a fannoni kamar zaman lafiya, tsaro, shugabanci, zuba jari, ilimi, matasa, lafiya, da ababen more rayuwa.

Kasancewarta masaukin sansanonin sojin Amurka, Faransa, China, Japan, da wasu ƙasashen waje, Djibouti tana amfani da waɗannan dangantaka wajen cigaban ƙasa—gina tashoshin jiragen ruwa, dabarun jigila, makamashi, da walwalar yankin—wannan na nuna yadda kwanciyar hankali na siyasa ke ba da damar cigaba mai ɗorewa.

A cikin gida, cigaban siyasar Djibouti—ko da akwai ƙalubale—yana ba da kyawun hasashe a wani yanki da ake samun juyin mulki a-kai‑a-kai, da sauyin mulki mai cike da rashin jituwa, ko rikice‑rikice masu tsawo.

Ta hanyar kiyaye tsari a cikin gida, ƙasar ta zama misali na kwanciyar hankali a matakin yanki wanda hakan ke ƙarfafa amincinta a matsayin mai sasanci kuma mahaɗa.

Matsayi mai adalci kan Gaza

Djibouti ta kuma ɗauki mataki mai aiki a zahiri kan batun Falasɗinu. Ta yi maraba da yarjejeniyar tsagaita-wuta ta Gaza, tana yaba wa ƙoƙarin Amurka, Qatar, Masar, da Turkiyya wajen tabbatar da tsagaita wuta wuta, buɗe hanyar jinƙai, da sakin fursunoni.

Shugaba Ismail Omar Guelleh ya yi kira da a aiwatar da cikakken shirin don tabbatar da zaman lafiya na dindindin, da sauƙin hanyoyin jinƙai, da bin tafarkin gaskiya don kai wa zuwa mafita ta samar da ƙasashe biyu.

Tsayayyen matsayin Djibouti yana ƙarfafa matsayar Afirka gabaɗaya: dole zaman lafiya ya fifita damar taimakon jinƙai, musayar fursunoni, da mafita mai yiwuwa ta samar da ƙasashe biyu yayin da ake girmama haƙƙokin Falasɗinu da burin ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta.

Misalin Djibouti cike yake da darussa. A yankin kusurwar Afrika, inda illar ƙarancin tsaro da rikici ta munana, ikon Djibouti na sasantawa ya samar da damarmakin tattaunawa, da tabbatar da dangantakar ƙasashen duniya cikin daidaito.

Ƙaramar ƙasa ce da ke taka yin tasiri fiye da girmanta idan diflomasiyya ta kasance mai ɗorewa, amintacce, kuma tushenta a cikin kwanciyar hankali na cikin gida.

Kusurwar Afirka ta Gabas yana ci gaba da kasancewa mara tabbas, yaƙi a Sudan na iya bazuwa zuwa yankuna, taƙaddama tsakanin Habasha da Eritrea tana nan, rashin tsaro a Bahar Maliya yana barazana ga kasuwancin duniya, yayin da matsin yanayi ke ƙara tsananta rikicin jinƙai.

Djibouti ba za ta iya magance waɗannan ƙalubale ita kaɗai ba, amma muryarta a matsayin mahaɗa kuma mai sasanci ba za a iya maye gurbin ta ba.

Ta hanyar tallafawa sasancin da Tarayyar Afirka ke jagoranta, da amincewa da tsarin tsagaita-wuta a Gaza, da kuma yin fafutuka don samun damar taimakon jinƙai a Sudan, Djibouti ta ayyana kanta a matsayin mai sasanci, kuma abar misalin a fannin kwanciyar hankali, inda dangantaka take iya daidaiciya dangantaka da manyan ƙasashen duniya don ƙara tasirinta fiye da iyakokin ƙasar.

Marubuciyar, Hafsa Abdiwahab Sheikh, 'yar jarida ce mai zaman-kanta kuma mai bincike wadda ke mai da hankali kan harkokin siyasar Gabashin Afirka.

Togaciya: Ra'ayoyin da marubuciyar ta bayyana ba lallai su nuna ra’ayin TRT Afrika ba, kuma ba sa wakiltar manufofin edita ko ra'ayoyin tashar ba.