China ta ce tana adawa mai "ƙarfi" ga yunƙurin Amurka na amfani da addini da ‘yancin ɗan’adam "wajen tsoma baki a harkokin Nijeriya” bayan Donald Trump ya yi barazanar yiwuwar kai hari Nijeriya kan zargin yi wa Kiristoci kisan gilla.
Beijing "tana nuna adawa mai ƙarfi ga ko wace ƙasa [da ke] fakewa da addini da ‘yancin ɗan’adam a matsayin hujjar tsoma baki a harkokin cikin gida na sauran ƙasashe da kuma yin barazanar takunkumi da fin ƙarfi kan wasu ƙasashe," in ji mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China Mao Ning yayin wani taron manema labarai a Beijing.

"A matsayinmu na muhimmiyar abokiyar hulɗar Nijeriya, China tana goyon bayan gwamnatin Nijeriya wajen jagorantar al'umarta a kan hanyar ci-gaban da ya fi dacewa da yanayin ƙasar, in ji ta.
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin soji kan Nijeriya ranar Asabar kan zargin yi wa Kiristoci kisan gilla,” bayan iƙirarin cewa addinin Kiristanci na fuskantar “ƙalubale mai iya shafe shi” a Nijeriya yayin da yake zargin "masu kaifin kishin addinin Musulunci " da "kashe mutane masu yawa."









