Shugaban Amurka Donald Trump ranar Asabar ya umarci Ma'aikatar Yaƙi ta ƙasar ta soma shirye-shiryen yiwuwar kai hari Nijeriya bayan da ya yi zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a ƙasar.
Trump ya bayar da umarnin ne a saƙon da ya wallafa a shafinsa na Truth Social kwana guda bayan ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla 3,100 a Nijeriya ba tare da ya bayyana takamaimai inda ya samu waɗannan alƙaluma ba.
“Muddin gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da dukkan tallafin da take bai wa Nijeriya nan-take, kuma mai yiwuwa za ta shiga wannan ƙasƙantacciyar ƙasar, cike da ƙarfin gwiwa domin kawar da 'yan ta'adda masu kaifin kishin Musulinci waɗanda ke yin wannan ta’asa,” in ji Trump.
Shugaban na Amurka ya ƙara da cewa: ”Ina bayar da umarni ga Ma'aikatar Yaƙinmu ta yi shiri domin yiwuwar ɗaukar mataki. Idan muka kai hari, zai kasance mai sauri da kaifi kuma daɗi, kamar dai yadda ‘yan ta’adda suke kai hari kan ababen ƙaunarmu Kiristoci.”
‘Yancin yin addini da haƙuri
Hakan na faruwa ne kwana guda bayan shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa Nijeriya tana nan daram a matsayin ƙasar da ake mulkin dimokuraɗiyya, wadda kundin tsarin mulkinta ke tabbatar da ‘yancin yin addini da haƙuri tsakanin mabambantan addinai.
A martanin da ya yi wa Trump, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa tun lokacin da gwamnatinsa ta hau mulki a shekarar 2023, tana ci gaba da gudanar da tattaunawa da duka shugabannin Kiristoci da Musulmai domin ƙarfafa haɗin kai da magance matsalolin tsaro da ke shafar ‘yan ƙasa daga kowane yanki da addini.
“Nijeriya tana nan daram a matsayin ƙasa mai dimokuraɗiyya wadda kundin tsarin mulkinta ke tabbatar da ‘yancin yin addini,” in ji Tinubu.
“Tun daga 2023, gwamnatinmu tana gudanar da tattaunawa sosai da shugabannin addinai na Kiristanci da Musulunci, tare da ci gaba da magance matsalolin tsaro da ke shafar jama’a daga addinai daban-daban da yankuna.”
Shugaban ƙasar ya ce, duk wani bayani da ke nuna cewa Nijeriya ƙasa ce mai fama da tsatsauran ra’ayin addini, ba ya nuna ainihin gaskiyar abin da ke faruwa a ƙasa, kuma ba ya la’akari da ƙoƙarin gwamnati wajen tabbatar da ‘yancin yin addini da ra’ayi ga kowa da kowa.
“‘Yancin addini da haƙuri suna daga cikin ginshiƙanmu kuma za su ci gaba da kasancewa haka,” in ji Tinubu. “Nijeriya na adawa da keta ‘yancin addini, kuma ba ta goyon bayan hakan.”









