An kama Chabi Yayi, ɗan tsohon shugaban Benin Thomas Boni Yayi wanda a yanzu babban ɗan adawa ne. An kama shi ne a safiyar Lahadi a gidansa, in ji wasu daga cikin 'yan uwansa.
Ba a bayar da dalilin kama shi ba, inda kamen ke zuwa mako guda bayan yunƙurin juyin mulki da aka yi a ƙasar.
"A wannan lokaci, ba mu san abin da ake zarginsa da shi ba," in ji wani daga cikin 'yan uwansa a tattaunawarsa da kamfanin dillancin labarai na AFP.
"Ba mu san ko hakan na da alaka da abubuwan da suka faru a ranar Lahadin da ta gabata ba," in ji wani na kusa da shi, kuma mamba na jam'iyyar Democrats, babbar jam'iyyar adawa, wacce Yayi ke shugabanta.
An kama mutane da dama kan yunƙurin juyin mulki
Thomas Boni Yayi ya yi Allah wadai da yunƙurin juyin mulkin da aka yi a cikin wani jawabi na bidiyo, kwanaki biyu bayan haka.
An yi kamen wasu tun bayan yunƙurin juyin mulkin na 7 ga Disamba, ciki har da wasu masu ruwa da tsaki a yunƙurin juyin mulkin da tsohon ministan tsaro da kuma wani babban ɗan adawa Candide Azannai, wanda yansanda suka kama bisa zargin “ƙulla makirci ga ƙasa da kuma rura tawaye a ƙasar.”
Wasu daga cikin waɗanda suka shirya yunƙurin juyin mulkin, ciki har da shugaban su Laftanan Kolonel Pascal Tigri, har yanzu ba a kama su ba.












