DUNIYA
2 minti karatu
Rundunar Sojin Ruwan Pakistan ta kama mugwayen ƙwayoyi na dala biliyan ɗaya a Tekun Arebiya
An kama wasu jiragen ruwa guda biyu da ba su da shaidar ƙasa, ɗauke da ƙwayar crystal meth da hodar iblis, kamar yadda rundunar hadin gwiwar teku da Amurka ke jagoranta ta faɗa.
Rundunar Sojin Ruwan Pakistan ta kama mugwayen ƙwayoyi na dala biliyan ɗaya a Tekun Arebiya
An gwada miyagun ƙwayoyin da aka kama sannan daga baya aka lalata su, in ji sanarwar. / Reuters Archive
7 awanni baya

Rundunar Sojin Ruwa ta Pakistan ta kama miyagun ƙwayoyi da kuɗinsu ya kusa dala biliyan $972 a Tekun Arebiya, in ji Rundunar Hadin Gwiwar Jiragen Ruwa ta Amurka (CMF).

CMF ta bayyana a cikin wata sanarwa ranar Talata cewa jirgin ruwa na sojin Pakistan, PNS Yarmook ne ya gudanar da aikin, wanda yake cikin ƙungiyar haɗin gwiwa ta Saudiyya, CTF 150, a karkashin aikin AL MASMAK.

"A cikin awanni 48, PNS Yarmook ta gudanar da bincike kan jiragen ruwa biyu; babu ɗayansu da ke amfani da tsarin Automatic Identification System (AIS) ko kuma suna da wata alamar waje, kuma an gano cewa babu wata ƙasa da ke da'awar mallakarsu," in ji sanarwar.

A ranar 18 ga Oktoba, ma'aikatan jirgin sun shiga jirgin ruwa na farko inda suka kama fiye da tan biyu na crystal methamphetamine (ICE) mai darajar dala miliyan 822.4.

Kasa da kwanaki biyu bayan haka, sai suka sake kama wani jirgin ruwa dauke da kilo 350 na ICE mai darajar dala miliyan $140 da kuma kilo 50 na koken mai darajar dala miliyan $10, a cewar sanarwar.

An gwada miyagun ƙwayoyin da aka kama sannan daga baya aka lalata su, in ji sanarwar.

Sai dai CMF ba ta bayyana ainihin wurin da aka kama miyagun ƙwayoyin ba.

"Nasarar wannan aiki mai maƙasudi ya nuna mahimmancin haɗin gwiwar ƙasashen duniya," in ji Commodore Fahad Aljoiad na Rundunar Sojin Ruwa ta Saudiyya, wanda shi ne kwamandan CTF 150.

"PNS Yarmook ta samu ɗaya daga cikin mafi nasarar kama miyagun ƙwayoyi a tarihin CMF, wanda hakan ya samo asali ne daga ƙwarewa da haɗin kai na rundunonin sojojin ruwa a cikin wannan ƙungiya," ya ƙara da cewa.

Aikin AL MASMAK, wanda aka fara a ranar 16 ga Oktoba, ya haɗa da haɗin kai daga Pakistan, Saudiyya, Faransa, Spain, da Amurka.

Rundunar Hadin Gwiwar Jiragen Ruwa, wadda ta ƙunshi ƙasashe 47 masu haɗin gwiwa, tana aiki don tabbatar da bin dokokin ruwa na duniya, da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a cikin murabba'in mil miliyan 3.2 na mahimman hanyoyin ruwa.