Ƙasar Benin da maƙociyarta Jamhuriyar Nijar sun kori jakadun juna a wani mataki da masana diflomasiyya ke kallo a matsayin ci gaba da taɓarɓarewar alaƙa da ke tsakanin ƙasashen biyu na Yammacin Afirka waɗanda ke maƙotaka da juna.
Bayanai sun nuna cewa hukumomi a Cotonou ne suka soma ayyana wasu jami’an jakadancin Nijar a Benin a matsayin waɗanda ba sa maraba da ci gaba da zamansu a ƙasar.
Rahotanni sun ce jami’an jakadancin na Nijar sun fice daga ƙasar ranar Alhamis, 1 ga watan Janairu.
Nan-take hukumomi a Yamai suka kori jami’an jakadancin Benin daga Nijar, lamarin da ya sa Benin ta sanar cewa daga ranar Litinin ɗin nan za ta rufe ofishin jakadancinta a Yamai.
Ƙasashen biyu su shafe fiye da shekaru biyu suna zaman doya da manja tun bayan juyin mulkin soji a Nijar da ya kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023.
Nijar ta sha yin zargin cewa Benin na son dagula lamura a cikin ƙasarta, wani zargi da mahukunta a birnin Cotonou suka musanta.
Wannan sabuwar dambarwa na zuwa ne wata guda bayan yunƙurin juyin mulki da sojoji suka yi a Benin, wanda shugaban ƙasar ya yi zargin cewa akwai hannun wasu ƙasashen waje, ko da yake bai ambaci sunan kowace ƙasa ba.
Nijar ta yi ƙawance da Burkina Faso da Mali, maƙwabta biyu da suke ƙarƙashin mulkin soji kuma suna ci gaba da aiwatar da manufofin bai-ɗaya na cigaban ƙasashensu, ciki har da ƙaddamar da rundunar soji ta ƙasashen uku da buɗe gidan talbijin da sauransu.
Dukkanin ƙasashen uku sun fita daga Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), wadda Benin ke cikinta, inda suka kafa wata ƙungiyar haɗin kai da ake kira Alliance of Sahel States (AES).













