| Hausa
TATTALIN ARZIKI
3 minti karatu
Hukumar SEC ta Nijeriya ta amince da tsarin rabon hannayen-jarin matatar Dangote
Matakin zai ta bai wa kamfanin Dangote Petroleum Refinery and Petrochemicals FZE damar fara rabon hannayen-jarin ga masu zuba jari.
Hukumar SEC ta Nijeriya ta amince da tsarin rabon hannayen-jarin matatar Dangote
Hukumar SEC ta Najeriya ta amince da tsarin rabon hannayen jarin matatar Dangote / Reuters (Wire)
 

Hukumar Kula da Kasuwannin Hannayen-Jari ta Nijeriya (SEC) ta amince da tsarin rabon hannayen-jarin kamfanin matatar mai ta Dangote, bayan samun gagarumin zuba jari a matatar a karon farko.

Wasu majiyoyi uku da ke da masaniya kan lamarin sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa hukumar ta amince da wannan mataki ne a ranar Litinin, 23 ga watan Nuwamba, bayan shafe makonni ana jiran mataki na gaba.

Wannan amincewar za ta bai wa matatar Dangote damar fara rarraba hannayen-jarin ga waɗanda suka zuba jari.

Haka kuma, kamfanin ya nemi amincewar hukumar domin ƙara yawan hannayen-jarin da yake son sayarwa da kashi 30 cikin 100, sakamakon yadda buƙatar masu zuba jari ta zarce adadin hannayen-jarin da aka shirya sayarwa da kusan ninki uku.

Masu AlakaTRT Afrika - Mutane daga kasashe 120 na duniya ciki har da na Afirka 54 sun sayin hannayen jari a Matatar Dangote

A watan Satumba ne kamfanin ya buɗe sayar da hannayen-jarinsa ga jama'a inda ya rufe a watan Oktoba kana ya nemi tara kusan naira tiriliyan 2.15, kwatankwacin dala biliyan 1.6, ta hanyar sayar da hannayen-jari biliyan 4.1 kan naira 525 kowane.

Kuma mafi ƙanƙantar adadin hannayen-jarin da mutum zai iya saya shi ne guda 10, wanda kuɗinsa ya kai naira 5,250. Hakan ya ba da dama ga masu ƙaramin ƙarfi su ma a dama da su ta manhajojin hada-hadar kuɗi da dillalan hannayen-jari da aka amince da su.

An gina matatar mai ta Dangote a yankin Lekki Free Zone da ke wajen birnin Legas, kan kuɗi da aka ƙiyasta sun kai dala biliyan 20. Matatar ta fara aiki a shekarar 2024, inda ta zama ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin samar da man fetur a Nijeriya.

Matatar tana da ƙarfin tace gangar ɗanyen mai 650,000 a kowace rana, duk da cewa ta taɓa samar da ganga 700,000 a rana.

Nan da shekarar 2029, kamfanin ya ce yana da shirin kara ƙarfin tace man zuwa ganga miliyan 1.4 a kullum.

Matatar na samar da man fetur, da dizal, da man jiragen sama da sauran kayayyakin da ake amfani da su a masana'antu, waɗanda take sayarwa a Nijeriya da kasuwannin ketare.

Kazalika, karuwar bukatar kayayyakin man fetur a kasuwannin duniya, musamman a kasashen Yammacin Turai, sun taimaka wajen ƙara yawan fitar da kayayyakin matatar zuwa kasashen waje, sakamakon tangarɗar samar da makamashi da yakin Iran ya haddasa, kamar yadda Reuters ta ruwaito.

Aliko Dangote ya kuma bayyana cewa kamfanin na iya fadada hannayen jarin matatar zuwa wata kasuwar hada-hadar hannayen-jari ta biyu a Amurka cikin shekaru uku zuwa huɗu masu zuwa.

Ana sa ran wannan hannayen jarin na matatar Dangote zai zama wani babban mataki ga kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Nijeriya, ta hanyar bai wa 'yan ƙasa damar mallakar wani ɓangare a babbar masana'antar makamashi ta cikin gida.