Cikin shekaru biyu a jere, tsarin kalandar karatu a Nijar ya fuskanci tsaiko sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da kuma ambaliya da suka tilasta wa gwamnati jinkirta buɗe makarantu a faɗin ƙasar.
A wata sanarwa da ofishin babban sakataren gwamnatin ƙasar ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana cewa an jinkirta shekarar karatu ta 2025-2026 da mako biyu, wato daga ranar 1 ga Oktoba zuwa 15 ga watan Oktoba, kamar yadda jaridar Actu Niger ta rawaito.
Sanarwar wadda babban sakataren Mahamane Roufal Laouali ya sanya wa hannu, ta ce matakin ya shafi ɗalibai kusan miliyan uku a faɗin ƙasar.
Hukumomi a ƙasar sun bayyana cewa, ɗage lokacin buɗe makarantu a Nijar ya zama dole saboda yanayin damina mai tsawo da aka samu, lamarin da ya sanya makarantu ba sa aiki kuma ajujuwa da dama sun cika da ruwa ko kuma suna buƙatar gyara cikin gaggawa.
An umarci gwamanoni da hakimai da jami’an ilimi su haɗa kai domin gyara makarantun gabanin sabuwar ranar da aka sanya ta buɗe makarantu a faɗin ƙasar.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da yanayin damina ke kawo cikas ga tsarin kalandar karatu a Nijar ba. A shekarar 2024, sai da ambaliyar ruwa ta tilasta wa hukumomi jinkirta soma shekarar karatu daga 2 ga watan Oktoba zuwa 28 ga Oktoba.
Hakan ya biyo bayan lalacewar makaratu da dama ko kuma mayar da su wuraren samun mafaka ga iyalai da suka rasa matsugunansu.
Kazalika ɗage lokacin buɗe makarantun ya daɗa ƙara matsin da tsarin ilimin Nijar ke ciki a ƙasar, inda a bana ake sa ran samun ɗalibai kusan miliyan uku.
Adadin ɗaliban dai ya nuna matsalolin da ake fuskanta kamar rashin isassun ajujuwa, da cunkoso a makarantu da kuma ƙarancin malamai.