Ƙungiyar Likitoci ta Sudan a ranar Asabar ta ce, mutane bakwai sun rasu a wani harin da jirgi maras matuƙi na rundunar Rapid Support Forces (RSF) ya kai a wata fitacciyar kasuwa a Kudancin Kordofan.
Ƙungiyar ta ce adadin mutanen da suka mutu a harin ranar Alhamis a kasuwar Dilling ya kai bakwai, yayin da 32 suka jikkata.
A cikin waɗanda suka mutu akwai yara uku da mata biyu, kamar yadda ƙungiyar ta ce inda ta ƙara da cewa mafi yawan waɗanda suka jikkata mata ne da yara kuma da yawa daga cikin waɗanda suka ji raunukan na cikin mawuyacin hali.
Ƙungiyar ta yi Allah wadai da “kisan kiyashin”, tana bayyana harin a matsayin babbar keta doka ta jinƙai ta duniya da kuma laifi a kan farar-hula marasa makamai.
Ƙarar ƙazantar lamarin
Ƙungiyar ta ce kai hari kan unguwanni na zama, kasuwanni da taron farar hula alama ce ta ƙara ƙazantar lamarin wanda ke ƙara azabtar da farar-hula da rage ƙoƙarin kare su.
Ƙungiyar ta ɗora alhakin harin da asarar rayukan farar-hula ga kwamandojin RSF, tana cewa an kai harin ne dagangan zuwa cibiyoyin farar-hula.
Ta yi kira kan al'ummar duniya, Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam da su saka baki don kare farar-hula, tilasta kawo ƙarshen hare-hare kan wuraren da mutane ke taruwa da kawo ƙarshen ƙawanyar da aka yi wa Dilling.
Ƙungiyar ta yi gargaɗi kan cewa Dilling na shiga mataki na uku na yunwa bayan an katse isar abinci sakamakon ƙawanyar da aka yi.
Hare-haren jiragen sama marasa matuƙa
RSF ba ta yi tsokaci nan da nan ba. Amma a ranar Juma'a, rahotannin kafofin watsa labarai sun ambaci majiyoyi da suka ce mutane biyar sun mutu kuma 25 suka jikkata a wani harin jirgin RSF a kasuwar Dilling.
Hukumomi sun sha zargin RSF da kai hare-hare da jiragen sama marasa matuki kan wuraren farar hula, ciki har da tashoshin wutar lantarki da sauran ababen more rayuwa a garuruwan arewa da gabas.
Biranen Kadugli da Dilling suna ƙarƙashin ƙawanyar RSF da ƙungiyar Sudan People's Liberation Movement-North (SPLM-N) tun farkon watannin yaƙin fiye da shekaru biyu da suka wuce, inda suke fuskantar ƙarin hare-haren jirage marasa matuƙa.
A 'yan makonnin baya-bayan nan, jihohin Kordofan guda uku — Arewa, Yamma da Kudu — sun sha tsananin fada tsakanin sojoji da RSF, abin da ya jawo 'gudun hijira' na dubban fararen-hula.
Dubban mutane sun mutu a yaƙi
Daga cikin jihohin Sudan 18, RSF na rike da dukkan biyar na yankin Darfur a yamma, ban da wasu sassan arewa na Arewacin Darfur da ke ƙarƙashin ikon sojoji. Sojoji kuma suna rike da mafi yawan yankuna na sauran jihohi 13 a kudu, arewa, gabas da tsakiyar ƙasar, ciki har da babban birnin Khartoum.
Rikicin tsakanin sojoji da RSF, wanda ya fara a Afrilun 2023, ya yi sanadin mutuwar dubban mutane da tilasta miliyoyi barin gidajensu.












