NIJERIYA
2 minti karatu
Dangote na shirin sayar da kashi 10 cikin 100 na hannayen-jarin matatar mansa
Dangote ya ce kamfanin man Nijeriya NNPC zai iya ƙara yawan hannayen-jarinsa a matatar bayan ya rage su zuwa kashi 7.2 cikin 100, amma sai mataki na gaba na haɓaka matatar ya kankama.
Dangote na shirin sayar da kashi 10 cikin 100 na hannayen-jarin matatar mansa
A halin yanzu dai matatar man Dangote tana da ƙarfin iya tace ganganr mai 650,000 ne a ko wace rana / TRT Afrika English
21 awanni baya

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana shirin matatar mansa na sayar da kashi 5 zuwa 10 cikin 100 na hannayen-jarinta a kasuwar hannayen-jarin Nijeriya a shekara mai zuwa.

Ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da S&P Global.

Dangote ya ce matakin zai yi kama da irin matakan da kamfanin simintin  Dangote da kamfanin Suga na Dangote suka ɗauka.

“Ba ma son mu riƙe fiye da [hannayen-jari] kashi 65 zuwa kashi 70 cikin 100,” a cewar Dangote.

Ya ƙara da cewa za a gabatar da hannayen-jarin a kasuwa ne a hankali bisa ga sha’awar masu zuba jari da kuma zurfin kasuwar.

Mai masana’antun ya ce rukunin kamfanoninsa yana kuma tunanin dabarar haɗin gwiwa da kamfanonin Gabas Ta Tsakiya domin faɗaɗa matatar da kuma wani sabon aikin samar da wata matata a China.

“Ra’ayin kasuwancinmu zai sauya. Yanzu maimakon mu kasance 100 bisa 100 na Dangote, za mu kasance muna da abokan tarayya,” in ji shi.

Dangote ya ce kamfanin man Nijeriya NNPC zai iya ƙara yawan hannayen-jarinsa a matatar bayan da ya rage su zuwa kashi 7.2 cikin 100, amma sai mataki na gaba na haɓaka matatar ya kankama.

“Ina son na nuna abin da matatar za ta iya yi, sannan za mu zauna mu tattauna,”  in ji shugaban rukunin kamfanonin.

Kazalika, matatar ta yi shelar shirye-shirye na ƙara yawan man da za ta rinƙa tacewa zuwa gangar mai miliyan 1.4 a ko wace rana, wani matakin da zai zarce na matatar da ta fi girma a duniya wadda take tace gangar mai miliyan 1.36 a ko wace rana da ke Jamnagar, a Indiya.

“A watan Yuli, Dangote ya bayyana shirye-shirye na faɗaɗa matatar daga ganga 650,000 da take tacewa a yanzu zuwa tace gangar mai a 700,000 a ko wace rana zuwa ƙarshen shekara,” in ji S&P Global.

“A halin yanzu, manufar ita ce [ta] kai ga [tace gangar mai miliyan 1.4 a ko wace rana, inda ba a bayyana wa’adin cim ma hakan ba, wani matakin da zai zarce na matatar da ta fi girma a duniya mai tace gangar mai miliyan  1.36 a ko wace rana da ke Jamnagar, a  Indiya.”