Rwanda da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka ta jagoranta a ranar Juma’a, wanda ta haifar da fatan kawo ƙarshen rikicin da ya kashe dubban mutane kuma ya raba dubban ɗaruruwan mutane da muhallansu kawo yanzu a bana.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya karɓi ministocin harkokin wajen ƙasashen biyu a Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka da ke birnin Washington don sanya hannu kan yarjejeniyar.
Washington ta sanar a watan da ya gabata cewa wannan yarjejeniyar zaman lafiya za ta bai wa kamfanonin Amurka da na Yammacin duniya damar zuba biliyoyin daloli a ma’adanan Kongo da ayyukan gina abubuwan more rayuwa a ƙasashen biyu, ciki har da sarrafa ma’adanai a Rwanda.
Massad Boulos, babban mai ba da shawara ga Shugaba Donald Trump kan harkokin Afirka, ya bayyana cewa yarjejeniyar ta haɗa da “janye matakan kariya daga Rwanda.”


















