An sanya Chadi a matsayin ƙasar Afirka mafi kura da hazo a shekarar 2025, inda yawan ƙananan barbashi masu hatsari a cikin iska ya haura yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta ba da iyakance, kamar yadda bincike ya nuna a ranar Talata.
Kamfanin sa ido kan ingancin iska na Switzerland masi suna IQAir a cikin rahotonsa na shekara-shekara ya bayyana cewa ƙasashe da yankuna 13 sun kiyaye matsakaicin matakan PM2.5 a ma'aunin WHO na ƙasa da microgram 5 a kowane cubic mita a bara, kari sama da kasshe akwai a shekarar 2024.
Jimilla, ƙasashe 130 daga cikin ƙasashe 143 da aka yi bincike a kan su sun kasa cika ƙa'idar WHO. Pakistan, Bangladesh da Tajikistan su ne manyan uku a jerin waɗanda suka fi gurɓata muhalli.
Chadi, ƙasa mafi yawan hazo da kura a shekarar 2024, ta kasance ta huɗu a shekarar 2025.
Yankin Bodele na arewacin Chadi ya kasancewa daya daga wurare mafiya kadawar iska a ban kasa kuma ana daukar sa a matsayin wajen da ya fi ko’ina samar da kura a duniya.
A watan Maris din shekarar da ta gabata, Amurka ta rufe wani shirin sa ido na duniya wanda ya tattara bayanan gurɓataccen yanayi da aka tattara daga manya da kananan ofisoshin jakadancinta, tana mai ambaton dalilan karancin kasafin kuɗi.
"Rasa bayanan a watan Maris ya sa ya zama kamar an sami raguwar matakan PM2.5 (a Chadi), amma gaskiyar magana ita ce ba mu sani ba," in ji Christi Chester Schroeder, babban marubucin rahoton IQAir.
Garin da yanayinsa ya fi kowane gurbace wa
Birnin Loni na India ne birni mafi gurɓacewa a duniya a shekarar 2025, inda matsakaicin ma'aunin PM2.5 ya kai microgram 112.5, sai Hotan a yankin Xinjiang na arewa maso yammacin China da microgram 109.6 a matsayi na biyu.
Biranen duniya 25 mafi gurɓacewa duk suna cikin India, Pakistan da China.
Kashi 14% ne kawai na biranen duniya suka cika ƙa'idar WHO a shekarar 2025, wanda suka ragu daga kashi 17% a shekarar da ta gabata, inda gobarar daji ta Canada ta ƙara yawan PM2.5 a faɗin Amurka da kuma Turai.
Daga cikin ƙasashen da suka cika ƙa'idar a shekarar 2025 akwai Australia, Iceland, Estonia da Panama.
A Laos, Cambodia da Indonesia duk an samu rahoton raguwar PM2.5 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, madalla ga yanayin La Nina mai danshi da iska mai ƙarfi.
Mongolia ta shaida matsakaicin yawan ma'aunin PM2.5 da ya ragu daga kashi 31% zuwa microgram 17.8 a kowane cubic mita guda.
A jimlace,a kasashe 75 an bayar da rahoton samun raguwar matakin PM2.5 a shekarar 2025 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata ta 2024, inda wasu kasashen 54 suka sami matsakaici mai yawa, in ji IQAir.












