Amaren Gaza: Matan da yaƙin Isra’ila ya mayar zawarawa rabi da rabi
A Jabalia, arewacin Gaza, fararen rigunn aure na mata na ci gaba da zama a rataye, alamun auren da ba za a yi shi ba har abada.
Amaren Gaza: Matan da yaƙin Isra’ila ya mayar zawarawa rabi da rabi
A Gaza, matan Falasdinawa na kallon yadda burinsu na aure ke dusashewa a karkashin buraguzan gine-gine da bakin ciki, inda ake kashe angwaye da wadanda aka yi musu baiko. Zobunan baiko, tufafi da bukukuwa sun zama alamun bakin ciki da sace makoma.
18 Agusta 2025

A Gaza, sautin farin ciki na zaghroota - gudar bikin aure da ake yi a a da don nuna farin ciki - ya dushe. A madadin hakan: sai karar hare-hare ta sama, karar shawagin jirage marasa matuƙa, da kukan iyalai a wajen makoki.

Bikin aure ya zama ba kasafai ba a yanzu. Hatta wadanda suka yi kokarin fara sabuwar rayuwa, burinsu ya gagara cim mawa.

Rugujewar tattalin arziƙi, tsoro a koyaushe, da baƙin ciki sun tilasta wa samari da ‘yan mata da yawa dakatar da shirin aure.

Ga matan Falasdinawa da ke shirin amarce wa, a yanzu kwanakin aure sun zama abubuwan tuna wa kawai. Kafin Oktoban 2023, bukukuwan aure a Gaza sun kasance bukukuwa masu ban sha'awa.

Tun daga daren henna  wanda amarya, kawayenta da ‘yan uwa da dangi ke halarta, zuwa taron zaffen na ango da abokansa - jerin gwanon raye-raye da wake-wake na 'yan uwa da abokan arziki a yayin daukar amarya daga gidan iyayenta - bukukuwa ne masu kayatarwa da nishadantarwa.

Gwamman wuraren bikin aure da aka gina sun zama na musamman a Gaza, wurare irin su Pearl Palace da Lighthouse Hall da ke unguwar al-Rimal, wurin taro na Al-Nour da ke Nuseirat, kuma, uwa uba, Princess Palace da ke kan titin Al-Sina’a a birnin Gaza duk suna da kayatarwa.

A yau, zauren bikin aure na Lighthouse yana kwance a karkashin baraguzan ginin, wanda hare-haren jiragen Isra'ila suka rusa.

Hare-Haren na Isra’ila kuma sun lalata wasu wuraren sosai, kamar sauran gine-gine 130,000 da aka mayar da su baraguzai.

Wasu dakunan taron, kamar Rose Hall da ke Tal Al-Hawa, an mayar da su matsugunai ga iyalai da aka raba da matsugunansu a Shujaiya da Zeitoun.

Maimakon tebura da ke lullube da yaduka masu kyawun gani, a yanzu wajen na lullube da barguna da katifu.

Rushe-Rushen sun tilasta wa saurayi da buduwar, waɗanda har yanzu suke manne da soyayya - su maye gurbin manyan bukukuwan aure tare da ‘yan kananan bukukuwa a cikin gidajen da har yanzu ke tsaye, ko a tantunan ‘yan gudun hijira.

Bukukuwna baiko, da a baya suke da girma da nisadantarwa amma da samun baki ‘yan kadan, a yanzu sun zama kananan taruka da ake yi cikin tsiri da fargabar fuskantar hari.

Soyaya bayan tsagaita wuta na wucin gadi

Ola Abdel Rabbo, mai shekaru 22, dalibin injiniyancin lantarki, ta samu yin baiko da Naseem Abu Subha a watan Fabrairu yayin tsagaita wuta na wucin gadi da Isra'ila ta yi a Gaza.

Matasan sun haɗu juna a yayin da suke nazarin kwas ɗin tsara yanar gizo kuma nan take kamu da son juna.

A wajen liyafar baikon da suka yi a gidan wani dan uwansu da ke Deir al Balah, a cikin rashin daga sauti, Naseem ya saka zoben zinare na mahaifiyarsa a yatsan Ola.

"Naseem bai iya siya min kayan al'adar bikin aure na shabka ba [wani setin zinare da ya kunshi sarka, dan kunne da awarwaro], saboda ba shi da kuɗi kuma shagunan sayar da zinare sun rufe," Ola ta tunatar. "Ya yi alkawarin zai saya min da zarar yakin ya kare."

An bai wa Naseem aiki a matsayin mai tsara manhaja a Birtaniya, kuma matasan da ke son juna na da kyakkyawan fata.

Naseem ya dan samu kayan ci da sha da aka yi da fulawa daga masu bayar da agaji, inda matasan biyu a wajen bikin baikon nasu suka samu halartar ‘yan uwa da abokay da suka tsifa a yankin.

Don bikin aurensu, sun yi shirin sayen kek daga ɗaya daga cikin mashahuran gidajen burodi na Gaza, kamar Badri da Shagon Haniya da ke Rimal.

Yayin da Abu Majed, wani gogagge wajen yin kek da gasa burodi a unguwar, yana tarbar masu shirin yin aure cikin murmushi, yana tambayar su, "Kuna son ken din ku ya za,a ruwan hoda kamar soyayyar ku, ko kuma fari kamar niyyarku?"

A yanzu kamshin vanilla ya daina cika Rimal. Maimakon haka, waɗanda suka tsira daga kisan kiyashin suna tambayae kawai: “Akwai garin fulawa?”

Har yanzu, Abu Majed ya kasance mai kyakkyawan fata: "Lokacin da wannan yaƙin ya zo karshe, zan yi ado da kek na farko da zaatar (wani ganyen Falasɗinawa na gargajiya mai kamshi) don zama abin tunatarwa ga al’adar da muka gada".

Tuna baya marar dadi

A wajen bikin baikonsu, Ola ta sanya rigar da ta dinka shekarun baya, fara da ruwan hoda da aka saya daga wani dan kasuwa a titin Omar Al-Mukhtar.

Ta tuno Naseem yana kallon ta cikin wannan rigar, murmushinsa na haska wa. A hankali aka kunna wakokin soyayya a wayar wani. Wannan lokacin yana ci gaba da rayuwa a kwakwalwarta - tunanin da take ɗauke da shi ita kaɗai a yanzu.

Bayan 'yan watanni, ranar 30 ga Yuni, a gidan shan shayi na bakin teku na Al Baqa, Naseem ya bayar da umarnin a kawo wa Ola abinci; ya sani a zuciya. Kofi na Turkiyya, sukari kadan.

Ya rubuta wani abu a kan shimfidar teburin sannan ya tura shi a hankali zuwa ga wadda yake shirin aura, Ga abinda ya rubuta: “Idan suka tambaye ka dalilin da ya sa kake son ta, ka ce domin ita kaɗai ce ta bar ka ka manta da karar shawagin jirage.”

Bayan Naseem ya dauki hotonsu tare a wayarsa, sai wani hari ta sama ya afka cikin wajen shan shayin.

Dukkan su sun fadi ƙasa. Kafar Ola na zubar jini, Naseem na kwance a gefenta ba ya motsi.

Ma’aikatan jiyya sun garzaya da su asibiti, amma bayan sa’o’i, dangin Ola sun tabbatar da mata da labari mafi muni: Naseem ya mutu.

Ta ce: "A ƙarshe sun ƙyale ni in gan shi. Ya yi kyau sosai kamar cikakken wata dan kwanaki 15."

Karyewar zuciyar da Ola ta samu ɗaya daga cikin irin sa da yawa ne. A gidajen da ke fadin Gaza, akwai ‘yan matan da ke shirin aure inda a yanzu sai tunanin mazan da ba za su taba aura ba, kamar Aseel Al-Ashqar, ita ma irin wannan kaddara ce ta same ta.

Kananan bukukuwan baiko, zukata masu karfi

A garin Gaza, dangin Aseel sun gudanar da wata ‘yar karamar walima a gidan wani dan uwanta ita da Ahmed al-Sahhar, makonni uku kacal kafin a fara yakin 7 ga Oktoba.

Matasan biyu sun cika da kyakkyawan fata, irin wanda kawai masu ƙaunar juna ne ke ji.

Ahmed, mai shekaru 28, likita, yana zaune a wani gini da ke gefen titi daura da gidan su Aseel, mai shekaru 26, kuma sau da yawa ta kan yi shiru tana kallon sa daga barandarta yayin da ya dawo daga aiki a matsayin likitan hakori a wani karamin asibitin unguwa. Daga karshe ya aika manyansa su nema masa auren ta kamar yadda al’ada ta tanada.

A ranar baikonsu, Aseel ta gyara gashinta gaban wani qaramin madubi sannan ta daura hijabinta a tsanake, sannan ta saka wani kwalli da ta adana domin wannan rana.

Ta shafa jan baki mai ruwan hoda da ta saya shekara daya da ta gabata daga titin Al-Wahda, a wani shago da shi ma a yanzu an rusa shi.

Da a ce kudi ya ba ta dama, da an yi mata kwalliya da gyara mata gashi a wuraren kwalliya da ke Rimal, kamar a Lamset Nisreen Salon, ko Rabab Styles da ke Shujaiya.

Aseel ta ajiye hotunan bikin baikon a wayarta. A kwanakin da suka biyo baya ta kan koma tana kallon su don sake jin dadin taron.

Makonni kadan bayan haka, bayan da aka fara yaƙin, wani hari da jiragen Isra’ila suka kai wa gidansu da ke Shujaiah ya ruguje ginin gaba ɗaya, kuma an tilasta wa iyalinta ƙaura zuwa Rafah.

Yayin gudun hijira, yayin da take rike da hannun mahaifiyarta suna gudu, wayarta ta fadi. Shin ko tana karkashin baraguzai? A gefen hanya ta fadi? Ba ta sani ba.

"Ba ni da sauran hoton da zan tabbatar da cewa zan zama amarya… amma ina tuna komai a cikin zuciyata, yadda Ahmed ya kalle ni da yadda hannuna ya yi karkarwa a yayin da na sanya zobe."

Ahmed ya ki barin Arewacin Gaza.

"Yana aiki tsakanin Asibitin Al-Awda da kuma Kamal Adwan. Ya ki ya bar marasa lafiya da wadanda suka jikkata a wurin, duk da cewa hare-hare ta sama na karuwa da sauri a yankin," kamar yadda Aseel ya shaida wa TRT World.

A ranar 21 ga Nuwamban 2023, yayin da Ahmed ke aiki a Jabalia, wani hari da Isra'ila ta kai ya fada ka hawa na uku da na hudu na Al-Awda. Ya rasu tare da wasu abokan aikinsa guda biyu.

Aseel ta ce kwanaki da yawa ba ta ji daga Ahmed ba, kuma makwabciyarta ce ta kawo mata labarin mutuwar.

Cikin kuka ta ce, “Na yi awanni da yawa ban iya yin magana ko kuka ba, na yi matukar kaduwa.”

Ta kara da cewa, "Ba mu san cewa burinmu na yin aure zai wargaje ba, kuma zan rasa Ahmed har abada."

Kamar yadda Aseel ke fama da rashin saurayinta, sauran samari da ‘yan mata na fuskantar raunin soyayya a karkashin kawanya.

An daga ranar baiko, juriyar soyayya

A watan Janairu, Ibrahim Abu Shaaban da Laila Ashour ‘yan yankinn Khan Younis, wadanda shekarunsu ba su wuce ashirin da dan wani abu ba, sun yi baiko bayan shafe shekaru biyar suna shan soyayya. Matasan sun hadu a jami'a amma sun kasa yin aure sai da suka kammala karatu, sannan Ibrahim ma ya samu aiki.

Sun yi niyyar yin baiko a ƙarshen 2023, amma yaƙin ya jinkirta shirin nasu.

Shekara guda da fara yaƙin, Ibrahim ya gaya wa Laila cewa su daina jira, kawai su yi baiko domin yana so ya kasance tare da ita a kowanne hali.

Ya fada mata, "Ba sai kin sanya min farar riga ba don na san ke ce amaryar zuciyata, ki zauna lafiya, sauran kuma za su biyo baya."

Rigunan amare sun kasance mafarki a Gaza. Ma'aurata da suke tururuwar zuwa kantin Retaj akan titin Al-Wahda da ke Rimal, kantin da ke cike da kayayyaki da aka shigo da su daga Turkiyya.

A nan ne babban tela, Abu Samer, yake, wanda ya shahara da sauya fasalin kowace riga don dace wa da kowacce amarya.

Ya kan ce: "Kowacce rigar amarya tana bayar da labari, kuma aikina shi ne in rubuta farin ciki da zare da allura."

Kwanaki hudu bayan fara yakin Isra'ila a Gaza, an kai hari kan titin Al-Wahda, kuma ginin Retaj ya ruguje. Fararen rigunan masu tsafta, sun zama toka.

Hoto mai ban tsoro aka dinga yada wa a shafukan sada zumunta na yanar gizo: rigar da ke rataye a cikin tarkace, kura ta lulluɓe ta. Abu Samer ya samu munanan raunuka inda aka kai shi kasar Masar domin yi masa magani.

Ga yawancin masu shirin zama amare, kallon wannan rigar kaɗai na snaya su jin kamar suna kallon mudubin rayuwarsu, an dakatar da mafarki daga zama gaske, suna jiran tsammani a yayin da ake ta shan wahala. Laila na daya daga cikin su.

Wata rana da daddare makonni bayan yi musu baiko, Laila tana tsaye saman soron gidansu tana kokarin samun layin sadarwar yanar gizo, sai ta samu sako ta wayarta daga saurayinta.

Yana cewa, "Yaƙin ya jinkirta baikonmu; bai jinkirta soyayyarmu ba. Ina jira, komai tsawon lokaci."

A ranar 11 ga Yuli, 2025, yayin da yake zaune a kofar gidansu a Deir al Balah tare da dan uwansa, wani harbi ta sama daga Isra'ila ya bugi wuyan Ibrahim. Ya mutu nan take.

Laila ta kasa yin magana saboda rashin da ta yi, sai ta baiwa dan uwan Ibrahim, Dr Areej Abu Shaaban, ya bayar da labarinta: “Mahaifin Ibrahim bai binne shi ba nan da nan, sai da ya ajiye gawarsa a cikin dakinsu ya bude fuskarsa, suka tsaya a gabansa suna kallon sa har washegari, mahaifinsa ya ce ya so Ibrahim ya bar gidan a matsayin ango.

Waɗannan labarun kaɗan ne kawai a cikin ɗaruruwa, duk da haka sun zama shaidar gaskiyar da babu wani hari ta sama da zai iya goge ta: zuciyar ɗan adam, har ma a cikin tsananin duhu, na ci gaba da nuna so da ƙauna.

Rumbun Labarai
Yadda ɗaliban Nijeriya suka samu zantawa da ‘yar-sama-jannati da ke Tashar ISS a sararin samaniya
Yadda dafa abinci na haɗin gwiwa a Somaliya ke ciyar da ɗaruruwan Falasɗinawa a Gaza
Hilda Baci: Fitacciyar mai girki ta Nijeriya ta dafa buhu 200 na shinkafa a yunƙurin kafa tarihi
Sabon nazarin WHO da ke shawartar a daina dukan yara da nufin gyaran tarbiyyarsu
Yadda ƙasaitaccen bikin 'yar hamshakin attajirin Nijeriya Femi Otedola, Temi ya ɗau hankali
Hotunan yadda dubban Musulmai a ƙasashen duniya suka yi murnar Maulidin Annabi
Ranar Hausa ta Duniya ta 2025 ta ƙayatar da gagarumin biki a Daura
Manufar bai ɗaya ta tsare harshe ta hade kawunan al’ummar Songhay-Zarma-Dendi
Ɗan Nijeriya ya kafa tarihi bayan ya gabatar da shirye-shiryen rediyo mafi tsawo a tarihi
Yadda bikin Rahama Sadau ya zo da mamaki amma ya samu yabo
Hotunan yadda ake tashin talakawa masu kwana a titi a birnin Washington na Amurka
Hijirar tsuntsaye: Afrika na tattaro kan duniya wajen ceto muhimman fadamu don biliyoyin tsuntsaye
Tsutsar Mopane: Daddaɗan abincin Namibia da ake ci tsawon zamanai
Maryam Bukar Alhanislam: 'Yar Nijeriyar da ta zama jakadiyar zaman lafiyar MDD ta farko a duniya
Dalilan da suka sa ake buƙatar mutane su samu abokai na zahiri a yayin da intanet ke jawo kaɗaitaka
Nairobi Birdman: Matashin da ke abota da tsuntsaye a Kenya
Yadda birai suka addabi wani gari a Afirka ta Kudu da "sata da ƙwace"
Abin da ya sa Kabul zai iya zama babban birni na farko da zai fuskanci matsalar rashin ruwa a duniya
Bikin Wasannin Al’adu Karo na 7 ya farfado da hadin kan al’adu, iyalai da ma duniya
Waiwaye kan tarihin Aikin Hajjin Annabta da yadda ake gudanar da shi