Wata matashiya mawaƙiya da ta kai matsayin shahara bayan ta bayyana a shirin ‘The Voice Nigeria’ a shekarar 2021 tana barci a gidanta da ke Abuja a ƙarshen makon da ya gabata lokacin da abin da ba a zata ba ya faru. Wani maciji ya shiga gidanta ya cije ta.
Ifunanya Nwangene, mai shekaru 26, ta mutu cikin 'yan awanni. Ba wai kawai daga gubar macijin da ke ratsa jininta ba, har ma da mummunan tsarin lafiya da ya kasa magance matsalar cikin gaggawa. Asibiti na farko da ta yi gaggawar zuwa an ce ba shi da maganin dafin macijin.
Bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta ya nuna wani mai kama maciji yana cire macijin daga gidanta yayin da mazauna yankin cikin firgici suka dinga ihu suna cewa "Maciji ne!" ga shi nan.
Ifunanya ta ja hankalin wadanda ta ke burgewa tare da muryarta a wakokin jazz, opera, kiɗan gargajiya, da kuma ruhi. Mawakiyar, wacce aka horar da ita a fannin fasahar gine-gine, tana shirin yin wasan kwaikwayo na farko a ƙarshen wannan shekarar.
Mutuwarta ta tilasta wa 'yan Nijeriya fuskantar wata gaskiya mai ban haushi: cizon maciji ya kasance wata matsala ta gaggawa ta lafiyar jama'a da aka yi watsi da ita, kuma karancin magani yana ci gaba da jawo asarar rayuka har ma a babban birnin ƙasar.
Matsalar da aka yi biris da ita
Najeriya na samun kusan mutane 20,000 da ke fuskantar cizon macizai kowace shekara, a cewar kiyasin ma'aikatar lafiya daga shekarar 2021.
Kimanin mutane 2,000 daga cikin wannan adadi na ras arayukansu, yayin da sama da mutane 1,700 da suka tsira ke fama da yankakken hannu ko nakasa ta dindindin.
Kwararru sun ce rikicin ya ci gaba da ta'azzara, ba a ba su kulawar da ta kamata ba har sai da ya fara shafar manyan mutane sannan aka fara waiuwawayar sa.
Likitan dabbobi a Najeriya Dr Abubakar Balla ya yi imanin cewa raunin tsarin da ake da shi wajen samun magani ya karu a tsawon shekaru.
"Cizon maciji rashin lafiya ce ta gaggawa da ke bukatar kulawar likita, duk da haka gibin rashin magani yana ci gaba da karuwa," Balla ya fada wa TRT Afrika. "Babbar matsalar ita ce inganci da dacewa da maganin macizai da ake samu a Nijeriya.
Kasar ta cika da maganin cizon macizai da aka shigo da su daga India, amma maganin dafin macizai zai fi yin aiki mafi kyau idan aka samar da shi duba ga nau'in macizai da ake samu a yankin da za a kai shi."
Yin amfani da maganin dafin macizai da aka samar daga nau'ikan da ba na 7yankin da za a yi amfann da shi bana rage sakamakon maganin, in ji shi.
"Ba mu da nau'in macizai na India a nan. Don haka, idan maganin kashe dafi bai yi daidai da nau'in dafi na gida ba, ana iya rage tasirinsa idan aka gamu da mummunan dafi."
Asibitin gwamnati da Ifunanya ta mutu ya musanta zarge-zargen cewa babu maganin kashe dafin a matsayin zance marar tushe.
Matsalar nahiya baki daya
Cizon maciji ya kasance babbar barazana ga lafiya a yankin kudu da hamadar Sahara. Kiyasi ya nuna cewa ana cizon mutane har miliyan daya kowace shekara a yankin, inda ake samun mace-mace tsakanin 7,000 zuwa 20,000 a kowace shekara.
Alkaluman suna da wahalar tattarawa saboda raunin tsarin bayar da rahoto da kuma wadanda ma ba sa zuwa asibitoci bayan cizon.
A Yammacin Afirka kawai, ana kiyasta mutuwa sakamakon cizon maciji tsakanin 3,500 zuwa 5,400 a kowace shekara. A wani asibiti a Nijeriya, an yi wa cizon maciji 6,687 magani a cikin shekaru uku kacal.
A Burkina Faso, an rawaito samun cizon maciji 114,126 a duk fadin kasar tsawon shekaru biyar (2010-2014), a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).
A Najeriya, macijin gansheka ne ke yin kusan kashi 90% na cizon maciji kuma kusan kashi 60% na mace-mace, in ji ma'aikatar lafiya ta Najeriya a shekarar 2021.
Abin mamaki, asibitoci a yankunan da ke da hatsarin fuskantar cizon sau da yawa suna fama da rashin isasshen maganin dafin.
"Maganin dafin maciji yana da tsada kuma ba ya dadewa a ajje," in ji Balla ga TRT Afrika. "Asibitoci wani lokacin suna jinkirin adana adadi mai yawa saboda allurai na iya lalacewa ba tare da amfani da su ba.
Mutane da yawa da abin ya shafa a yankunan karkara suna fara neman maganin gargajiya, suna ganin ya fi rahusa ko kuma ya fi sauƙi.
Don haka, asibitoci suna ƙarewa da zubar da kayan da lokacin amfaninsu ya ƙare ba tare amfana da su ba."
Kuma wannan ba ya bayyana wuraren da ma ba su da maganin dafi kwata-kwata. Abokan Ifunanya sun shaida wa kafofin watsa labarai na gida cewa asibiti na farko mai zaman kansa da ta ziyarta sun bayar da shawarar ta nemi magani a wani wuri, inda suka ce ba su da maganin dafin.
Jinkirin janyo mutuwa
A ra’ayin Balla, dole ne a fara yin gyare-gyare cikin gaggawa tare da horar da likitoci.
"Dole ne a ske horar da likitoci, ba tare da la'akari da fannin da suka ƙware ba, musamman a yankunan da cizon maciji ya zama ruwan dare, kuma a koya musu shawo kan marar lafiyar da maciji ya sara nan da nan," in ji shi.
"Ya kamata a shigar da maganin cizon maciji na zamani cikin manhajar makarantun likitanci, kuma ci gaba da horar da ƙwararru yana da muhimmanci don gina ƙwarewa."
Balla ya kuma yi tsokaci da cewa dole ne Najeriya ta farfaɗo da saka hannun jari a cikin bincike da samar da maganin dafin maciji na gida don tabbatar da maganin cizon maciji na musamman ga nau'ikan macizan da ake da su a gida.
"Cibiyoyin kiwon lafiya na farko a yankunan da ake da macizai - ko da kuwa ba su da yawa - ya kamata a buƙaci su tanadi maganin dafin kuma su sami ma'aikata masu horon bayar da shi," in ji shi.
"Ya kamata a goyi bayan wannan doka don a sami magani lokacin da lamarin gaggawa ya afku."
WHO ta gano cewa ƙarancin damar samun maganin dafin mai inganci da kyawu a yankuna da yawa, musamman yankin kudu da hamadar Sahara, yana ingiza waɗanda abin ya shafa da yawa zuwa ga maganin gargajiya.
Rashin ingantattun kayan more rayuwa, talauci, ayyukan al'adu da raunin tsarin bayar da agajin gaggawa duk suna taimakawa wajen jinkirin isa ga samun kulawa mai kyau.
Da yawa daga cikin wadanda abin ya shafa suna fara neman masu maganin gargajiya kafin su je asibiti, yayin da wasu kuma ba za su iya samun sufuri cikin gaggawa ba. Wasu suna mutuwa kafin su isa asibiti mafi kusa.
Balla ya yi gargaɗin cewa ra'ayin da ake da shi na cewa cizon maciji yana faruwa ne kawai a yankunan karkara na iya zama batun ɓatar da mutane.
"Kamar yadda muka gani a cikin mummunar kddarar Ifunanya, macizai na iya shiga gidaje har ma a birane," in ji shi.
"Yawancin cibiyoyin birane a yau a baya dazuzzuka ne ko kuma daji. Yayin da ake lalata ko sauya muhalli, macizai na ƙaura kuma suna haɗuwa da mutane. Lambuna masu furenni da yawan beraye da gafiyu da kadangaru a birane da yawa na jawo hankalin macizai."
WHO ta yi gargaɗi akai-akai cewa bai kamata a sake ɗaukar cizon maciji a matsayin matsalar lafiya da aka yi watsi da ita ba.
Ga 'yan Nijeriya da yawa, mutuwar Ifunanya ta kawar da zaton da ake yi da shi cewa cizon maciji hatsari ne na karkara kuma ya fallasa matsalar da ke tattare da agajin gaggawa idan ya afku.














